Hotunan matashi mai shekaru 23 yayi wuf da fitacciyar 'yar siyasa mai shekaru 45
- Shekaru ba komai bane in dai akwai so da kauna, haka ne yasa jama'a da dama basu duban shekaru a soyayya
- Hakan ce kuwa ta faru da matashi dan Najeriya mai shekaru 23 mai suna Adam Dalla wanda ya aura 'yar siyasa mai shekaru 45
- 'Yan Najeriya a kafafen sada zumunta sun cika sashin tsokaci bayan ganin kyawawan hotunan masoyan na hakika
Matashi dan Najeriya mai shekaru 23 mai suna Adam Dalla ya aura fitacciyar 'yar siyasa a Adamawa mai suna Barista Jamila Babuba.
Kamar yadda wallafar da shafin @lindaikejiblogofficial yayi a Instagram, ma'auratan sun angwance a ranar 18 ga watan Mayun 2021 kuma zasu yi walimar aurensu ne a ranar 31 ga watan Mayun 2021.
KU KARANTA: Matasa sun kone mahaukaciya bayan kama ta da suka yi da makamai a Legas
Kyawawan hotuna da katin gayyatar liyafar bikin sun bazu a kafafen sada zumunta kuma jama'a sun matukar nuna sha'awarsu da wannan soyayya dake tsakanin ma'auratan.
KU KARANTA: Rikicin shugabanci: ISWAP sun kama kwamandojin Shekau, sun gana da wadanda suka yi mabaya'a
A yayin martani ga wallafar, wata ma'abociya amfani da Instagram mai suna @ju_sapphire ta rubuta: "Gareku maso son kirgar shekaru, ku cigaba da kirgawa. Zaku iya zuwa nawa nima. Shekaru ba komai bane, natsuwa ce kawai! Duk inda ka samu soyayya, je ka ka samu farin ciki. Ba zamu dawwama a duniya ba, don haka kayi rayuwa cike da morewa. Mutane zasu yi magana, amma waye ya damu."
@jagun_of_afrika kuwa tsokaci yayi da: "Ina taya ku murna... Natsuwa da farin ciki yafi maganganun jama'a"
@mavwills6 cewa tayi: "Anya wannan yaron, ko dai bashi da iyaye ne??"
@kokolet_natural cewa tayi: "Soyayya a Ethiopia, ina taya ku murna."
A wani labari na daban, jami'an 'yan sanda da kungiyar 'yan sa kai dake Hayin Daudu a garin Gusau na jihar Zamfara sun halaka 'yan bindiga 10 a ranar Litinin.
Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Muhammad Shehu, ya sanar da cewa 'yan sanda da 'yan sa kai sun gaggauta zuwa inda aka kira su sakamakon harin da 'yan bindigan ke kaiwa Hayin Daudu, Premium Times ta ruwaito.
"'Yan sandan da aka tura yankin Mada, sun hadu da wata kungiyar sa kai wurin karfe 11 na dare inda suka yi gaggawar zuwa Kauyen Hayin Daudu sakamakon kiran gaggawa da suka samu."
Asali: Legit.ng