Gwamnatin Zamfara ta tabbatar da ceto mutum 76 da aka sace a YarKatsina

Gwamnatin Zamfara ta tabbatar da ceto mutum 76 da aka sace a YarKatsina

- Gwamnatin Zamfara ta samu nasarar ceto mutum 76 daga hannun miyagu

- Gwamnatin ta yi ikirarin cewa ba ta biya kudin fansa ba

- Jihar Zamfara na cikin jihohin dake fama da matsalar tsaro a Arewacin Najeriya

Mutum saba'in da shida da aka yi garkuwa da su a garin Yarkatsina a karamar hukumar Bungudu na jihar Zamfara sun samu yanci, gwamnatin jihar ta tabbatar.

Gwamnatin jihar ta ce yan bindigan sun saki wadanda suka sace ne ba tare da biyan kudin fansa ba bayan sulhu da ita.

Mutanen da aka sace yawancinsu mata da yara ne.

Kwamishinan labarai na jihar Zamfara, Ibrahim Dosara, ya bayyana hakan, TVC ta ruwaito.

A cewarsa, an sakesu da yammacin Laraba kuma dukkansu ne.

DUBA NAN: Shugaban kasar Mali da Firai Ministansa sun yi murabus

Gwamnatin Zamfara ta tabbatar da ceto mutum 76 da aka sace a YarKatsina
Gwamnatin Zamfara ta tabbatar da ceto mutum 76 da aka sace a YarKatsina
Asali: Twitter

DUBA NAN: Gwamna Bala Muhammad ya halarci taron jin bahasi kan garambawul wa kundin tsarin mulki

A wani labarin kuwa, dakarun sojin rundunar Operation Hadin Kai sun kai samame garin Kurkareta na jihar Yobe inda suka cafke masu samarwa Boko Haram kayan aiki.

Kamar yadda Sahara Reporters ta bayyana, daraktan yada labarai na rundunar sojin kasa, Mohammed Yerima, ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba a Abuja.

Kamar yadda Yerima yace, wasu daga cikin abubuwan da aka samu yayin samamen da ya samu tallafin 'yan sa kan yankin sun hada da jarka 62 dankare da man fetur wadanda aka boye a gidaje da shaguna daban-daban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel