Hotunan gida mai ɗaki daya da ake bayar da shi haya kan N1.6m a Abuja ya jawo cece kuce

Hotunan gida mai ɗaki daya da ake bayar da shi haya kan N1.6m a Abuja ya jawo cece kuce

- Kudin hayar wani gida mai daki daya a yankin Gwarinpa da ke Abuja ya haddasa cece-kuce da dama a shafin Twitter

- Da yake sanya kudin hayar gidan na shekarar farko a kan N1.6m, dillalin gidan ya ce kudin sun hada da na dukkan kayan daki da na cikin gidan

- An kuma bayyana cewa duk abinda ke cikin gidan ya zama mallakin wanda ya kama hayar gidan bayan shekarar farko

Wani gida mai daki daya a Abuja wanda kudin hayar sa ya kai N1.6 miliyan ya sa mutane suna magana kan yadda aka tsara shi a shafukan sada zumunta.

Da yake wallafa hotunan gidan a shafin Twitter, shafin @comfortzone23 ya ce kudin hayar gidan shine N800,000 amma biyan farkon ya yi yawa ne saboda an hada kudin komai na gidan.

KU KARANTA KUMA: Burina shine in auri mata 20 - Mutumin da ya auri mata 12 ya haifar da cece-kuce a sabon bidiyo

Hotunan gida mai ɗaki daya da ake bayar da shi haya kan N16m a Abuja ya jawo cece kuce
Hotunan gida mai ɗaki daya da ake bayar da shi haya kan N16m a Abuja ya jawo cece kuce Hoto: @comfortzone23
Asali: Twitter

Hakanan ya bayyana cewa duk wanda ya biya kudin hayar toh kayan sun zama mallakinsa saboda wanda ya siya kayan a sabbinsu zai koma kasar waje da zama.

'Yan Najeriya da dakin ya birgesu sun tofa albarkacin bakunansu. Yayin da wasu ke son karin bayani, akwai wasu da suka yi korafi a kan girman dakin girkin.

Kalli wallafan a kasa:

KU KARANTA KUMA: Da dumi-duminsa: Tsohon dan takarar Shugaban kasa ya sauya sheka zuwa PDP gabannin 2023

Ga wasu daga cikin martanin jama’a a kasa:

@tam_godwin ya ce:

"Banɗaki wanda ya fi dakin girki girma."

@asaina ya ce:

"Ya kamata kicin din ya koma bandaki sannan bandaki ya koma kicin."

@omoba_007 ya ce:

"Bandaki ya fi kicin girma ... Masu gine-ginen Abuja."

@Chief_Moze ya ce:

"Wani irin mugunta ne wannan, babban bandaki tare da madaidaicin kicin. Kuskuren gini."

A wani labarin, fasinjoji masu tarin yawa sun nitse a yankin arewa maso yammacin Najeriya a ranar Laraba bayan tafkeken jirgin ruwa dauke da fasinja 160 ya kife a kogin Neja, jami'i mazaunin yankin ya tabbatar.

Jirgin ruwa da ya bar jihar Kebbi yana tunkarar yankin arewa maso yammacin jihar Kebbi ya fashe sannan ya nitse, Abdullahi Buhari Wara, hakimin Ngaski ya tabbatar.

"Tuni dai masu ceto suka fada kogin amma mutum 22 tare da gawar mutum daya suka iya tsamowa," Wara yace a yanzu kusan fasinjoji 140 ne babu duriyarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel