Matsalar tsaro: Sarkin Musulmi da Oonin Ife sun fadawa Buhari tilas ya canza dabarun yaki

Matsalar tsaro: Sarkin Musulmi da Oonin Ife sun fadawa Buhari tilas ya canza dabarun yaki

- Muhammad Sa’ad Abubakar III ya halarci taron da aka yi a kan batun tsaro

- ‘Yan Majalisar wakilai sun kira wani zama na musamman jiya a garin Abuja

- Sultan ya bukaci shugabanni su rage surutu, su tsaya suyi wa al’umma aiki

Mai alfarma Sultan na Sokoto, Sa’ad Abubakar III da Ooni na kasar Ife, Oba Adeyeye sun yi kira ga gwamnati ta sake dabara wajen yakar matsalar rashin tsaro.

Da suke magana jiya, manyan sarakunan sun bayyana cewa ba zai yiwu gwamnatin tarayya ta cigaba da amfani da dabara daya, ta na tunanin ta ga sauyi ba.

Jaridar The Nation ta ce Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci a rage surutu, a dage da aiki.

KU KARANTA: Buhari ya yi magana kan rashin tsaro

Sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa’ad Abubakar, da Sarkin kasar Ife sun yi jawabi ne wajen taron da majalisar wakilai ta kira a kan sha’anin tsaro.

Sultan yake cewa tun da ya zama Sarkin Musulmi shekaru 15 da suka wuce, ana yawon surutu, ba tare da an yi wani aiki tukuru da za a gani, kuma har a yaba ba.

“Mun yi ta magana. Mun yi magana a kungiyar gwamnonin Arewa; mun yi a taro na kasa. A watannin nan, mun yi ta zama irin wannan da shugabanni.”

“Yanzu ma ga mu, duk a kan abin da ya shafi tsaron kasa. Surutan sun isa.” Inji Sarkin Musulmi.

KU KARANTA: Sultan ya bukaci a fadawa Jama'a ina ake kai kudin sata

Matsalar tsaro: Sarkin Musulmi da Oonin Ife sun fadawa Buhari tilas ya canza dabarun yaki
Sultan da Sarkuna Hoto: @HrhBayero
Asali: Twitter

Sultan ya cigaba da cewa: “Mu tsaya muyi aiki; mu aikata abin da ake fada. Muna zama a nan, muna kara bata lokacin da ya kamata muyi aikin kirki ne.”

Basaraken ya yi kira a ji tsoron Allah; “Shugabanni suna yin wani abu. Sai suyi magana a waje, ayi masu tafi. Da an watse,, sai suyi watsi da abin da suka fada.”

The Cable ta ce Sultan ya bada shawarar ayi gyara a kan yadda ake amfani da kafafen sadarwan zamani, ya nuna ba ya goyon bayan a haramta amfani da su.

A makon nan ne aka ji wani 'dan majalisa na jihar Oyo, Hon. Ajibola ya kai karar Shugaba Muhammadu Buhari a kan irin ta'adin da ake yi mutanensa.

A cewar sa, masu garkuwa da mutane da gungun barayi sun addabi al’ummarsa, don haka ya bukaci ayi bincike a kama masu laifi, kuma a biya jama'a diyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng