Dalibai 100 Sun Yanke Jiki Sun Faɗi Bayan Shaƙar 'Guba' Yayin Rubuta Jarrabawa

Dalibai 100 Sun Yanke Jiki Sun Faɗi Bayan Shaƙar 'Guba' Yayin Rubuta Jarrabawa

- Daliban Kwallejin Lafiya da Kimiyya ta Ijero-Ekiti a jihar Ekiti kimanin 100 sun yanke jiki sun fadi yayin rubuta jarrabawa

- Hakan ya faru ne sakamakon feshin magani da jami'an hukumar kashe gobara na jihar ke yi a makarantar yayin rubuta jarrabawar

- Afkuwar hakan ya saka yan uwansu dalibai yin zanga-zanga da lalata wasu kayayyakin makaranta da motoccin malamai

Daliban Kwalejin Lafiya da KImiyya, Ijero-Ekiti, a ranar Laraba, sun shiga firgici, bayan abokan karatunsu kimanin 100 sun shaki wani abu da ake zargin guba ne yayin da ake yin feshin magani a makarantar.

The Punch ta ruwaito cewa daliban sun yanke jiki sun fadi ne yayin da ake rubuta jarrabawa a aji yayin da su kuma jami'an hukumar kashe gobara na jihar ke yin feshin magani.

Dalibai 100 Sun Yanke Jiki Sun Faɗi Bayan Shaƙar Guba Yayin Rubuta Jarrabawa
Dalibai 100 Sun Yanke Jiki Sun Faɗi Bayan Shaƙar Guba Yayin Rubuta Jarrabawa. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wata Sabuwa: Farashin Burodi Zai Yi Tashin Gwauron Zabi, Masu Gidajen Burodi Sun Sanar

Wani ganau da ya nemi a boye sunansa ya ce a kalla dalibai 100 ne suka yanke jiki suka fadi sakamakon shakar sinadarin kemikal din kuma an garzaya da su asibitoci a wajen makarantar.

An gano cewa wasu daliban da aka kai asibitin suna da ciwon matsalar numfashi ta asma hakan yasa suka samu matsala bayan shakar sinadarin.

Faruwar wannan lamarin ya fusata daliban inda suka nemi makarantar ta yi musu bayani game da afkuwar lamarin kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Sun yi zanga-zanga har ta kai ga sun lalata kayayaki da suka hada da ofisoshi, motoccin malamai da sauransu wadda hakan yasa malaman makarantar suka tsere.

KU KARANTA: An Rasa Rai Sakamakon Hatsarin Da Shugbannin PDP Suka Yi a Plateau

Kwamishinan lafiya na jihar Ekiti, Dr Banji Filani ya tabbatar da afkuwar lamarin amma ya ce a halin yanzu komai ya dai-daita.

Filani ya ce an kama wasu daga cikin jami'an hukumar kashe gobara na jihar kuma suna hannun yan sanda inda ake gudanar da cikkaken bincike.

A wani labarin daban, 'yan sanda a birnin tarayya Abuja sun kama Ahmad Isah, mai rajin kare hakkin bil adama kuma dan jarida, saboda shararawa wata mari da ake zargi da cin zarafin wata yarinya.

Isah, wanda aka fi sani da 'Ordinary President' ya dade yana gabatar da wani shirin rediyo da talabijin mai suna "Brektet Family".

Al'umma sun yi korafi a kansa ne bayan an gan shi cikin wani faifn bidiyo da BBC Africa Eye ta wallafa yana marin wata mata da ake zargin da cinnawa yar dan uwanta wuta a kai kan zarginta da maita.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel