An Rasa Rai Sakamakon Hatsarin Da Shugbannin PDP Suka Yi a Plateau

An Rasa Rai Sakamakon Hatsarin Da Shugbannin PDP Suka Yi a Plateau

- Sakatariyar kudi ta jam'iyyar PDP a jihar Plateau, Mrs Mary Adar Gar ta riga mu gidan gaskiya

- Gar ta rasu ne sakamakon hatsarin mota da ta yi tare da wasu shugabannin PDP a Plateau inda sauran suka jikkata

- Jam'iyyar ta PDP reshen jihar Plateau da ke shirin zaben kananan hukumomi ta dakatar da rali don karrama Gar da sauran da suka jikkata

An dakatar da ziyarar da jami'an jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ke kaiwa a Plateau ta Tsakiya sakamakon hatsarin mota da ya yi sanadin rasuwar sakatariyar kudi, Mrs Mary Adar Gar.

The Punch ta ruwaito cewa mummuna hatsarin ya auku ne a ranar Litinin da yamma a Mangu a lokacin da wata mota kirar Vectra ta yi karo da motar da ke dauke da shugabannin PDP da ke dawowa daga Shendam inda suka hallarci taron jam'iyyar na Plateau South.

An Rasa Rai Sakamakon Hatsarin Da Shugbannin PDP Suka Yi a Plateau
An Rasa Rai Sakamakon Hatsarin Da Shugbannin PDP Suka Yi a Plateau. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An Kama 'Likitan' Bogi Da Ke Shiga Daji Yana Yi Wa Ƴan Bindiga Aiki a Katsina

Ana yawon kai ziyarar ne gabanin zabukan kananan hukumomi da ke tafe a jihar a watan Oktoba.

Wani ganau, Timothy Pam, ya ce, "Karon da motoccin suka ya yi wurgi da sakatariyar kudin da ke zaune a bayan motar. An tabbatar da cewa ta rasu a yayin da aka kai ta Asibitin Koyarwa ta Jami'ar Jos. Direban Vectra din bai farfado ba a lokacin da na baro asibitin."

Mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Bitrus Golen, wanda shima hatsarin ta ritsa da shi amma ya tsira ya ce ikon Allah ne ya cece su.

KU KARANTA: NSCDC Ta Yi Ram Da Wasu Dillalan Miyagun Ƙwayoyi Biyu a Jigawa

Sakataren watsa labarai na PDP, John Akans, ya ce jam'iyyar ta soke rali da aka shirya yi na Central Zone a ranar Talata don karrama marigayiyar da wadanda suka jikkata sakamakon harin.

Da aka tuntube shi, jami'in hulda da jama'a na hukumar kiyayye haddura ta kasa, FRSC, Andrew Bala, ya ce zai yi bincike kan lamarin domin ba a shigar da batun ba a hukumance.

A wani labari daban, Ƴan bindiga sun kashe ƴan sa-kai 19 a ƙauyen Yartsakuwa a ƙaramar hukumar Rabah na jihar Sokoto kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin garin, wanda ya yi magana da majiyar Legit.ng a wayar tarho ya ce ƴan sa-kan sun rasa rayukansu ne yayin da suke ƙoƙarin daƙile harin da ƴan bindigan suka kaiwa garin.

Mazaunin garin, da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce yan bindigan sun kai hari ne ƙauyen misalin ƙarfe ɗaya na ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel