Sauya shekar gwamna Ayade zuwa APC ya girgiza mu kuma ya bamu kunya, Gwamnan Taraba

Sauya shekar gwamna Ayade zuwa APC ya girgiza mu kuma ya bamu kunya, Gwamnan Taraba

- Jam'iyyar PDP ta yi rashin babban jigo a jihar Cross Riba ranar Alhamis

- Uwar jam'iyyar ta rusa dukkan sauran shugabannin jam'iyyar dake jihar

- Wannan ne gwamnan kudu na biyu da ya koma APC tun bayan zaben 2019

Gwamna Darius Ishaku na jihar Taraba ya bayyana sauya shekar gwamnan Kross Riba, Ben Ayade, zuwa jam'iyar All Progressives Congress (APC) ya girgizasu kuma yayi matukar basu kunya.

Gwamna Ishaku ya bayyana hakan ne yayin hira da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawa da shugaban ma'aikatar Aso Rock, Farfesa Ibrahim Gambari ranar Juma'a, rahoton DT.

Ishaku yace: "Ba san abinda yake tunani ba, saboda mun yi matukar girgiza da fitarsa daga jam'iyyarmu zuwa APC, saboda dukkanmu na ganin PDP matsayin mafita daga APC."

"Kuma dukkan gwamnonin PDP na kokari sosai a jihohinsu. Amma ban san dalilin da ya sa ya koma APC ba."

Gwamnan yace wannan ba laifin kwamitin sulhu da dinke barakar jam'iyyar karkashin Saraki bane saboda mambobin kwamitin sun yi kokarin ganin cewa bai sauya sheka ba.

"Sun yi kokari sosai. Amma ya danganta da shawarar da mutum ya yanke ko abinda yake sa ran samu," yace.

DUBA NAN: FG ta yi sulhu tsakanin Kwadago da El-Rufa'i, an yi yarjejeniya

Sauya shekar gwamna Ayade zuwa APC ya girgiza mu kuma ya bamu kunya, Gwamnan Taraba
Sauya shekar gwamna Ayade zuwa APC ya girgiza mu kuma ya bamu kunya, Gwamnan Taraba Hoto: @IshakuDarius
Asali: Twitter

KU KARANTA: Isra’ila da Hamas Sun Amince Da Tsagaita Wuta Bayan Kwana 11 Ana Rikici

A bangare guda, wani rahoto da jaridar The Nation ta fitar ya nuna cewa akalla jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) 11 a jihar Ribas sun sauya sheka zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a cikin makon da ya gabata.

Yakin neman daukaka tsakanin tsohon gwamnan jihar da ministan sufuri, Rotimi Amaechi da wasu shugabannin jam'iyyar APC ya tarwatsa jam'iyyar.

Wannan ya ba shugabancin PDP dama don jan hankalin mambobin jam'iyyar adawa a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel