Ba Za Mu Lamunci Halasta Shan Tabar Wiwi Ba a Nigeria, NDLEA

Ba Za Mu Lamunci Halasta Shan Tabar Wiwi Ba a Nigeria, NDLEA

- Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya, NDLEA, ta ce bata goyon bayan halasta shan wiwi a kasar

- Buba Marwa, shugaban NDLEA na kasa ne ya bayyana hakan yayin taron tsaro da majalisar wakilai na tarayya ta shirya

- Marwa ya ce bincike da alkalluma sun nuna cewa shan miyagun kwayoyi na taka rawa wurin tunzura rashin tsaro

Shugaban hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi, NDLEA, Brig. Gen. Mohamed Buba Marwa (mai ritaya) ya yi gargadin cewa yunkurin da wasu ke yi na ganin an halasta amfani da wiwi zai janyo wa kasar koma baya a nasarar da ta samu wurin yaki da sha da safarar muggan kwayoyi.

Marwa ya yi wannan gargadin ne yayin jawabinsa wurin taron tsaro da majalisar wakilai na kasa ta shirya a ranar Laraba, Daily Trust ta ruwaito.

Ba Za Mu Lamunci Halasta Shan Tabar Wiwi Ba a Nigeria, NDLEA
Ba Za Mu Lamunci Halasta Shan Tabar Wiwi Ba a Nigeria, NDLEA. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: EFCC Ta Kama Hamshaƙin Ɗan Siyasa Kuma Ɗan Kasuwa a Neja

Ya ce alkalluman da ake da shi a yanzu da ya nuna yan Nigeria miliyan 10.6 ke shan wiwi ya isa darasi ga kasar.

A cewarsa, akwai kwakwarar alaka tsakanin shan miyagun kwayoyi da kallubalen tsaro a kasar.

"A halin yanzu babu abin da ya fi ciwa Nigeria tuwo a kwarya kamar matsalar tsaro. Tana daga cikin manyan kallubale idan ma ba ita bane mafi girma. Rashin tsaro babban matsala ne a yau da ta haifar da wasu matsaloli kamar tada kayan baya, yan bindiga, garkuwa da mutane, kisa, fashi, kisar ramuwar gayya da sauransu," wani sashi na jawabinsa.

KU KARANTA: An Kama 'Likitan' Bogi Da Ke Shiga Daji Yana Yi Wa Ƴan Bindiga Aiki a Katsina

Ya cigaba da cewa akwai kwakwarar alaka tsakanin shan miyagun kwayoyi da aikata laifuka.

Ya ce ana iya gani karara cewa babu yadda dan adam zai tashi yana aikata irin manyan laifukan da ake yi a kasar nan a baya bayan nan idan ba tun farko ya kausasa zuciyarsa da muggan kwayoyi ba.

Marwa ya kuma ce alkalluma da bayanai da aka tattara sun nuna cewa amfani da haramtattun kwayoyi na bada gudunmawa wurin tabarbarewar tsaro.

A wani labari daban, Ƴan bindiga sun kashe ƴan sa-kai 19 a ƙauyen Yartsakuwa a ƙaramar hukumar Rabah na jihar Sokoto kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin garin, wanda ya yi magana da majiyar Legit.ng a wayar tarho ya ce ƴan sa-kan sun rasa rayukansu ne yayin da suke ƙoƙarin daƙile harin da ƴan bindigan suka kaiwa garin.

Mazaunin garin, da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce yan bindigan sun kai hari ne ƙauyen misalin ƙarfe ɗaya na ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel