Jigawa: 'Yan sanda sun damke mutum 5 akan zargin lakadawa shugaban APC duka

Jigawa: 'Yan sanda sun damke mutum 5 akan zargin lakadawa shugaban APC duka

- 'Yan sandan jihar Jigawa sun cafke mutum 5 da ake zargi da hannu wurin lakadawa shugaban APC na Dutse duka

- Kamar yadda aka gano, sun kutsa sakateriyar jam'iyyar yayin da ake taro sannan suka dauka Malam Yakubu ta karfi da yaji

- Sun kai shi wani wuri inda suka masa duka sannan suka bukaci ya fitar da wanda suke so a matsayin dan takara

'Yan sandan jihar Jigawa sun cafke wasu mutum biyar da ake zargi da kaiwa Malam yakubu Ibrahim hari, shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Dutse.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Usman Gomna, ya tabbatar da kamen ga manema labarai a garin Dutse a ranar Laraba, The Nation ta ruwaito.

Kwamishinan 'yan sandan yayi bayanin cewa wadanda ake zargin sun kutsa sakateriyar jam'iyyar dake karamar hukumar yayin wani taro da aka yi a ranar Litinin inda suka saka karfin tuwo suka dauka shugaban jam'iyyar zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Kamar yadda yace, yayin da yake hannun maharansa sun tirsasa shi da ya bayyana dan takararsu a matsayin dan takara a zaben kananan hukumomi dake gabatowa a jihar.

KU KARANTA: Labarin Rashin Lafiyar Osinbajo: Fadar Shugaban Kasa ta Magantu

Jigawa: 'Yan sanda sun damke mutum 5 akan lakadawa shugaban karamar hukuma mugun duka
Jigawa: 'Yan sanda sun damke mutum 5 akan lakadawa shugaban karamar hukuma mugun duka. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

Kamafanin Dillancin Labaran Najeriya ya tattaro cewa wannan cigaban ya biyo bayan bayyana sunan 'yan takarar da zasu kara a zaben shugabannin kananan hukumomi 27 na fadin jihar.

An zargi cewa wasu daga cikin magoya bayan jam'iyyar tare da mambobi ne basu gamsu da sunayen wadanda aka bayyana ba domin takarar shugabancin karamar hukumar, Premium Times ta ruwaito.

Kwamishinan 'yan sandan jihar ya karyata jita-jitan dake yawo na cewa garkuwa aka yi da shugaban jam'iyyar.

"Wannan ba zancen garkuwa dashi bane saboda wadanda suka sacesa basu bukaci ko sisin kwabo ba kafin su sake shi.

"Rikicin na cikin gida ne wanda mu kuma muka basu shawarar da su sasanta cikin kwanciyar hankali.

“Amma duk da haka, 'yan sandan jihar sun damke wasu mutum biyar daga cikin 10 da ake zargi da yin wannan aika-aikar.

“Tuni 'yan sanda suka shiga al'amarin kuma zaman lafiya ya dawo yankin," cewar kwamishinan 'yan sandan.

Ya tabbatar da cewa nan babu dadewa 'yan sandan zasu cafke sauran mutum biyar da ake zargi da aika-aikar.

A wani labari na daban, Manjo Nura Hamza, daya daga cikin sojin da suka rasu a hatsarin jirgin sama na ranar Juma'a, 21 ga watan Mayun 2021 an san shi da taimakon marayu da gajiyayyu kamar yadda jama'a ke fadi.

Kamar yadda majiyoyi daban-daban suka tabbatar, ya shirya raba kayan makaranta da littatafai ga dalibai a makarantan Salim dake Kaduna a ranar 24 ga watan Mayu bayan kammala aikinsa a wata jihar arewa maso yamma.

Legit.ng ta ruwaito yadda jirgi Beechcraft 350 yayi hatsari a Kaduna yayin da dakarun sojin Najeriya ke ciki wadanda zasu halarci yayen sojoji a Zaria.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng