Jaja Wachuku: Jakadan Najeriya na farko da ya fara yaki da babancin launin fata a UN
Najeriya ta yi shugabanni nagari a daban-daban wadanda isarsu bata amfani kasar kadai ba, hatta wasu kasashe sai da ta shafa.
Jaja Wachuku, tsohon mai wakiltar Najeriya ne a majalisar dinkin duniya kuma shahararre ne. A wannan rahoton, Legit.ng ta tattaro abubuwa shida da ya dace ku sani game da dattijon mai nagarta.
1. Yayi yaki domin ceto rayuwar Nelson Mandela
A 1963 lokacin da aka yankewa shugaban kasar Afrika ta kudu da wasu mutum 12 hukuncin kisa, Face2FaceAfrica ta tattaro cewa Jaja yayi amfani da isarsa wurin ceto su.
Duk da daga baya an yanke musu hukuncin daurin rai da rai, amma hukuncin bai kai yadda kowa yake tsammani ba.
KU KARANTA: Mutum 2 sun fita da kumbo daga jirgin Janar Attahiru: Menene gaskiyar al'amarin?
KU KARANTA: Yadda na tsallake hatsarin jirgin sama da ya kashe Attahiru, Dan majalisar tarayya
2. Daga gidan sarauta ya fito
An haife shi a ranar 1 ga watan Janairun 1918, tsohon dan siyasan ya fito daga tsatson Sarki Josiah Ndubuisi Wachuku da sarauniya Rebecca ta kasar Ngwa.
Mai rajin kare hakkin dan adam din ya kasance mai jinin mayaka domin yadda mahaifiyarsa ta zamanto mace mai yaki da rashin adalci a lokacin rayuwarta.
3. Nasararsa ta farko
A 1979, ya samu nasarar da babu wani dan Najeriya da ya taba samu inda ya zama kakakin majalisar wakilai na farko.
Kamar hakan bai isa ba, shine jakaden farko kuma mai wakiltar Najeriya a majalisar dinkin duniya daga kasar nan na dindindin.
Wani rahoto da ba a tabbatar ba yace ya taba yin baccin karya a matsayin zanga-zanga kan wani tsokaci da aka taba yi yayin taro na wariyar launin fata.
4. Soyayyarsa ga iyalinsa da jama'arsa
Sunan matarsa Rhoda Idu Oona Onumonu kuma ya aureta a 1951. Sun samu haihuwar 'ya'ya biyar. A yayin yakin basasa, ya yi yaki saboda jama'arsa.
A jamhuriya ta biyu, ya kasance mai alaka mai karfi da majalisar dattawan Najeriya.
5. Mutum ne mai matukar hazaka
A lokacin da yake dalibi a kwaleji, yayi ta samun masu daukar nauyin karatunsa kuma kyaututtuka suna biyo baya. Irin gidan masu kudi da ya fito daga, ya taimaka masa wurin samun karatu mai inganci.
6. Rayuwarsa a jami'a
Daga cikin nasarorin da ya samu yayin da yake dalibi, ya wakilci jami'ar Dublin yayin wata mahawara tsakanin jami'o'i a 1943 wacce aka yi a jami'ar Durham, Wikipedia ta ruwaito.
Fadar shugaban kasa tayi martani ga wani rahoto dake bayyana cewa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo bashi da lafiya kuma an gan shi a asibitin Reddington dake Legas a ranar Asabar, 22 ga watan Mayu.
Kamar yadda Sahara Reporters suka ruwaito, ganin Osinbajo a asibitin ya janyo tashin hankula da kuma tambayoyi daban-daban na dalilin zuwan mataimakin shugaban kasan asibitin.
A yayin karin bayani, Sahara Reporters tace "Abinda yasa 'yan Najeriya suka damu da ganin mataimakin shugaban kasan a asibitin Reddington dake Legas shine ganin bai halarci jana'izar marigayi shugaban sojin kasa na Najeriya ba, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da sauran jami'ai 10 wadanda suka yi hatsarin jirgin sama a Kaduna."
Asali: Legit.ng