NSCDC Ta Yi Ram Da Wasu Dillalan Miyagun Ƙwayoyi Biyu a Jigawa

NSCDC Ta Yi Ram Da Wasu Dillalan Miyagun Ƙwayoyi Biyu a Jigawa

- Hukumar NSCDC ta samu nasarar kama wasu samari biyu a Jigawa masu safarar miyagun kwayoyi

- Jami’in hulda da jama’ar hukumar, Adamu Shehu ne ya sanar da manema labarai a Dutse ranar Talata

- A cewar Shehu, matasan suna baje kolin kwayoyin ne a kasuwar Kauyen Kanya Babba duk mako

Hukumar NSCDC ta jihar Jigawa ta kai samame a cikin jihar inda tayi nasarar damkar masu wasu matasa 2 masu safarar miyagun kwayoyi a karamar hukumar Babura, The Nation ta ruwaito.

Jami’in hulda da jama’an NSCDC, Adamu Shehu, ya tabbatar da kamen ga manema labarai a Dutse.

NSCDC Ta Kama Wasu Dillalan Miyagun Kwayoyi Biyu a Jigawa
NSCDC Ta Kama Wasu Dillalan Miyagun Kwayoyi Biyu a Jigawa. Hoto: @TheNationNews

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

DUBA WANNAN: An Sallami Malaman Makarantun Frimare 20 Daga Aiki a Niger

Kara karanta wannan

Guguwar NNPP na neman ratsa siyasar Kano, Shekarau da su Sumaila za su fice daga APC

A cewar Shehu, daya daga cikin matasan shekarunsa 20 dayan kuma 22 suna hannu bayan an kamasu suna baje kolinsu a kasuwar kauyen Kanya Babba da take ci duk mako.

“Don rage munanan ayyuka a cikin jihar, hukumar ta kai samame kasuwar kauyen Kanya Babba da takeci duk sati a karamar hukumar Babura.

“Jami’an sun kama wani matashi mai shekaru 20 wanda ake zargin yanada masaniya akan saye da sayarwar tabar Wiwi da sauran kayan maye.

“Bayan an kamashi ne aka samu nasarar kama dayan matashin mai shekaru 22 wanda shine babban mai safarar kayan mayen,” a cewar Shehu.

A cewarsa, an kamasu da kwayoyi 525 na ENZHEK-5, da kuma dayar D5 wacce akafi sani da ‘Yar Fara’, dauri 88 da wasu sunkuna na tabar wiwi, da robobin shalisho wacce akafi sani da Sholi duk daga hannunsu.

KU KARANTA: An Sallami Malaman Makarantun Frimare 20 Daga Aiki a Niger

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Tsagerun Kudu sun kone mota makare da shanu da ta taso daga Arewa

A cewar kakakin, an samu waya kirar itel, agogon hannu, kambu da kudi N14140 daga hannunsu.

A cewarsa, wadanda ake zargi da laifunkan sun amsa laifukansu kuma za a mikasu hannun NDLEA don a cigaba da bincike kuma a yanke musu hukunci.

“Shugaban hukumar NSCDC, Alhaji Garba Muhammad na jihar, ya bukaci hadinkan jama’a da suyu gaggawar sanar da hukumar duk wani aikin baraka da alfasha da suka gani don ayi gaggawar daukar mataki,” a cewar Shehu.

A wani labarin rahoton daban, gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike ya zargi tsohon gwamnan jihar Niger, Babangida Aliyu da zaman ɗan leƙen asiri da matsala ga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

Da ya ke magana a gidan gwamnati a Port Harcourt a ranar Litinin, Wike ya ce Aliyu mutum ne da ya daɗe yana yaudarar jam'iyyarsu ta PDP ya kuma yi mata zagon ƙasa an 2015, The Nation ta ruwaito. Wike Ya Ce Aliyu 'Ɗan Leƙen Asiri' Ne Kuma Alaƙaƙai Ne Ga PDP.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a Kano: Ganduje na yunkurin hana Jibrin ficewa daga jam’iyyar

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin martani kan wata hira da aka yi da Aliyu a jaridun ƙasa idan ya zargi Wike da ƙoƙarin mayar da kansa uban jam'iyya kuma kai mulkin kama karya a PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel