Soja da ya rasu a hatsarin jirgin sama ya shirya rabawa marayu kayan makaranta da littatafai

Soja da ya rasu a hatsarin jirgin sama ya shirya rabawa marayu kayan makaranta da littatafai

- Manjo Nura Hamza na daya daga cikin sojojin da suka rasu a hatsarin jirgin sama da aka yi a Kaduna

- Kafin nan, ya shirya rabawa marayu kayan makaranta da litattafai a garin Kaduna a yau Litinin, 24 ga watan Mayu

- Bayan taimakon marayu da aka san shi da shi, shine ya kafa asibitin Musulunci dake Kawo Kaduna

Manjo Nura Hamza, daya daga cikin sojin da suka rasu a hatsarin jirgin sama na ranar Juma'a, 21 ga watan Mayun 2021 an san shi da taimakon marayu da gajiyayyu kamar yadda jama'a ke fadi.

Kamar yadda majiyoyi daban-daban suka tabbatar, ya shirya raba kayan makaranta da littatafai ga dalibai a makarantan Salim dake Kaduna a ranar 24 ga watan Mayu bayan kammala aikinsa a wata jihar arewa maso yamma.

Legit.ng ta ruwaito yadda jirgi Beechcraft 350 yayi hatsari a Kaduna yayin da dakarun sojin Najeriya ke ciki wadanda zasu halarci yayen sojoji a Zaria.

KU KARANTA: Mutuwar Attahiru da sauran sojoji: Buhari yayi umarnin sauke tutoci na kwanaki 3

Hafsin soja da ya rasu a hatsarin jirgin sama ya shirya rabawa marayu kayan makaranta da littatafai
Hafsin soja da ya rasu a hatsarin jirgin sama ya shirya rabawa marayu kayan makaranta da littatafai. Hoto daga @Aliyu_Abubakar1
Asali: Twitter

Wadanda suka san Manjo Hamza sun ce, jami'in harkar kudi na shugaban sojin kasan Najeriya, marigayi Laftanal Janar Ibrahim Attahiru, ya shirya zuwa wata makaranta bayan kammala aikinsa.

Legit.ng ta tattaro cewa ya siya kayan makaranta da littatafai domin rabawa sabbin dalibai a wata makaranta ballantana marayu.

Marigayi Manjo Hamza ne ya kafa asibitin Musulunci dake Kawo, Kaduna. Asibitin dake duba mazauna jihar a kyauta.

Ya karanci fannin tattali a jami'ar Bayero dake Kano kuma ya kammala a 2002. Wasu daga cikin jama'ar da suka san shi sun cigaba da yabon kyawawan halayyarsa.

KU KARANTA: Hotunan ziyarar ta'aziyyar da Aisha Buhari ta kaiwa matar Janar Attahiru sun bayyana

Maidalan Kabi rubutawa yayi: "Manjo Nura Hamza, kai soja ne amma mai taimakon jama'a. Ayyukanka ga jama'ar yankinka da kasarka ba zasu shafe ba. Allah ya jikanka."

Aliyu Abubakar yace: "Manjo Nura Hamza, abokina ne kuma yana daga cikin wadanda suka rasu. Soja ne kuma nagari. Zamu iya cewa Allah ne ke badawa kuma yake karbar rayuwa. Allah ya gafartawa mamatan."

Muhammed Rabiu Idris Kura yace: “Allah ya jikanka Manjo Nura Hamza, wanda ya kafa asibitin Musulunci dake Kawo Kaduna. Allah ya yafe masa kura-kuransa.Ameen."

A wani labari na daban, a watan Satumban 2006, sojojin Najeriya da suka hada da janarori 10, laftanal kanal daya da wasu biyu sun rasu sakamakon hatsarin da Dornier 228-212 ya tafka a jihar Binuwai.

Sojojin na kan hanyarsu ta zuwa Obudu Cattle Ranch dake jihar Cross River, jaridar The Cable ta ruwaito.

Janarorin 10 da laftanal kanal din suna daga cikin kwamitin fadar shugaban kasa da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kafa domin gyaran rundunar sojin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel