Tallafin fetur: NNPC za ta saurari zaman Gwamnati da ‘Yan kwadago kafin a yanke farashi

Tallafin fetur: NNPC za ta saurari zaman Gwamnati da ‘Yan kwadago kafin a yanke farashi

- NNPC ta na jiran yadda zaman ‘Yan kwadago da Gwamnati zai kasance a yau

- Matsayar da aka cin ma a yau zai yi tasiri a kan yadda za a tsaida farashin fetur

- Kungiyar NLC ta ce za ta kawo maganar korar ma’aikata da ake yi a Kaduna

Hukumar mai na kasa watau NNPC ba ta tunanin cire tallafin man fetur a halin yanzu. Punch ta tabbatar da wannan a wani rahoto da ta fitar a ranar Talata.

Duk da shawarar da kungiyar gwamnonin Najeriya ta bada na cewa a janye tallafin man fetur da gaggawa, da alamun NNPC ba ta dauki wannan matakin ba.

NNPC ta na sauraron zaman da za ayi tsakanin gwamnatin tarayya da shugabannin ‘yan kwadago inda za a yanke matsaya a game da farashin mai.

KU KARANTA: Ministan mai ya ce 'yan Najeriya su saurari karin kudin fetur

Za ayi wannan zama ne a daren yau, 25 ga watan Mayu, 2021, inda daga karshe za a san ko gwamnatin tarayya za ta cigaba da biyan tallafin man fetur.

Shekaru kusan uku kenan NNPC ce kadai ta ke shigo da fetur, don haka ita ke daukar nauyin karin kudin da ake samu wajen saida fetur a gidajen mai.

Mataimakin shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero, ya shaida wa ‘yan jarida cewa za su zauna da gwamnatin tarayya a kan abin da ya shafi harkar farashin mai.

Kwamred Joe Ajaero ya kuma ce za su tabo maganar sallamar ma’aikatan da gwamnatin jihar Kaduna ta ke yi, wanda hakan ya jawo aka yi gajeren yajin-aiki.

KU KARANTA: Abin da ya sa Shugaban kasa Buhari ya janye tallafin mai – Sylva

NNPC ta na jiran Gwamnatin Buhari a kan batun kara farashin man fetur a Najeriya
Timipre sylva Hoto: saharareporters.com
Asali: UGC

An shafe kusan watanni uku ana jan daga a kan yadda za a saida litar man fetur a gidajen mai.

A baya, gwamnatin tarayya da ma’aikatar man fetur sun tabbatar da cewa za a bar farashin man fetur a yadda yake akalla har zuwa karshen watan nan na Yuni.

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC ya sake jaddada cewa ba za a kara farashin litan man fetur a watan Maris ba duk da tashin da farashin danyen man yayi.

Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta ƙara jaddada wa yan Najeriya cewa su shiryawa ƙarin farashin man fetur saboda matsin tattalin arziƙi da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel