Abin da ya sa Shugaban kasa Buhari ya janye tallafin mai – Timipre Sylva
Ganin irin rudanin da aka shiga, gwamnatin tarayya ta ma’aikatar man fetur ta fito ta bayyana abin da ya ke faruwa game da tashin farashin mai a Najeriya.
Karamin ministan mai na kasa, Cif Timipre Sylva, a wani jawabi da ya sa hannu a ranar Laraba, ya yi bayani dalla-dalla a game da tsarin gwamnatin shugaba Buhari a kan harkar mai.
Ministan ya ce gwamnati ba za ta iya cigaba da batar da tiriliyoyin kudi duk shekara da sunan tallafin man fetur ba, musamman ganin yadda talakawa ba su amfana da tsarin sosai.
A cewar ministan tarayyar, gwamnati ta tashi daga jagorar masu shigo da mai a Najeriya. “Amma za a tallafawa ‘yan kasuwa su karbi ragamar shigo da kayan man.”
Timipre Sylva ya ke cewa: “Wannan yana nufin daga yanzu ‘yan kasuwa ne za su rika bayyana yadda kudin litar man fetur zai kasance.”
“Kamar dai yadda aka saba yi a kasashen da aka cigaba, gwamnati za ta cigaba da aikinta na sa ido, wajen ganin cewa ‘yan kasuwa ba su tsawwala farashi ba.” Inji ministan.
Ma’aikatar mai za ta zama tamkar CBN wajen lura da aikin da bankuna su ke yi, misali ta hanyar lura da adadin ruwan da ake laftawa a kan bashi.
KU KARANTA: Gangar danyen fetur ya na kara tsada a kasuwannin Duniya
“Ana samun kayan mai ne daga danyen mai. Don haka farashin gangar danyen mai da kudin tacewa ya na tasiri wajen farashin da za a saida litar man fetur."
"A da lokacin da mai ya yi sama, gwamnati ta kan tabbatar cewa ‘yan Najeriya sun cigaba da amfana.”
Kwanakin tallafin man fetur ya zo karshe bisa dukkan alamu inda aka ji ministan ya na cewa ya zama dole ayi hakan a yanzu, saboda “Wannan ya wajaba ga duk gwamnati mai tunani.”
“Abin da ya sa Najeriya ta gaza jawo ‘yan kasuwa su zo su zuba jari shi ne harkar bada tallafin mai. Dole a samar da irin wannan kafa saboda a ga irin abin da ya faru a a harkar banki da jiragen sama.”
Gwamnati ta ce cire tallafin mai zai hana a rika biyan ‘yan kasuwa kudi a bagas, sannan zai kawo ayyukan yi, tare da gina abubuwan more rayuwa domin masu hannun jari za su shigo kasar.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng