Da Dumi-Duminsa: Annobar Cholera Ta Kashe Mutane 20 a Bauchi

Da Dumi-Duminsa: Annobar Cholera Ta Kashe Mutane 20 a Bauchi

- Cutar amai da gudawa wato Cholera ta yi sanadin rasuwar mutane 20 a Bauchi

- A kalla mutane 322 suka kamu da cutar tun bayan bullar ta a jikin wata matar aure a Afrilun 2021

- Kwamishinan lafiya na jihar Bauchi, Dr Aliyu Mohammed Maigoro ne ya bada wannan sanarwar

A kalla mutane 20 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon kamuwa ta annobar cutar Cholera (amai da gudawa) da ta barke a jihar Bauchi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A kalla mutane 322 ne aka ruwaito sun kamu da cutar da ta yadu a kananan hukumomi tara a jihar ta Bauchi.

DUBA WANNAN: Wike Ya Ce Aliyu 'Ɗan Leƙen Asiri' Ne Kuma Alaƙaƙai Ne Ga PDP

Da Duminsa: Cholera Na Yaduwa a Bauchi, Ta Kashe Mutum 20
Da Duminsa: Cholera Na Yaduwa a Bauchi, Ta Kashe Mutum 20
Asali: Original

Kwamishinan lafiya na jihar Bauchi, Dr Aliyu Mohammed Maigoro, shine ya bada wannan karin bayanin yayin taron manema labarai a ranar Talata.

KU KARANTA: Masu Zanga-Zanga Sun Tare Hanyar Abuja-Kaduna Kan Sace Mutum 30 Da Yan Bindiga Suka Yi

Maigoro ya yi bayanin cewa mara lafiya na farko da aka gano tana dauke da cutar, wata ce mai shekaru 37 kuma an kwantar da ita a babban asibiti Burra a ranar 24 ga watan Afrilun 2021 a karamar hukumar Ningi.

Bayan kwantar da ita ne sai aka gano akwai bullar cutar ta amai da gudawa a wasu garuruwa da ke makwabtaka da su kamar Sumaila da wasu kananan hukumomi a Kano da akwai yiwuwar daga Bauchi abin ya yadu kamar yadda The Nation ta ruwaito.

A wani labarin daban, 'yan sanda a birnin tarayya Abuja sun kama Ahmad Isah, mai rajin kare hakkin bil adama kuma dan jarida, saboda shararawa wata mari da ake zargi da cin zarafin wata yarinya.

Isah, wanda aka fi sani da 'Ordinary President' ya dade yana gabatar da wani shirin rediyo da talabijin mai suna "Brektet Family".

Al'umma sun yi korafi a kansa ne bayan an gan shi cikin wani faifn bidiyo da BBC Africa Eye ta wallafa yana marin wata mata da ake zargin da cinnawa yar dan uwanta wuta a kai kan zarginta da maita.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel