Mutum 2 sun fita da kumbo daga jirgin Janar Attahiru: Menene gaskiyar al'amarin?

Mutum 2 sun fita da kumbo daga jirgin Janar Attahiru: Menene gaskiyar al'amarin?

A ranar Asabar, 22 ga watan Mayun 2021, Daily Post ta ruwaito wani rahoto inda take ikirarin cewa wasu mutum biyu sun fita da kumbo daga jirgin da yayi hatsari da shugaban sojojin kasan Najeriya, Ibrahim Attahiru da sauran sojoji 10.

Rahoton ya kara da bayyana cewa mutanen biyu da suka fita da taimakon kumbon sun bace daga nan.

KU KARANTA: Rundunar sojin Najeriya ta sanar da ranar birne Janar Attahiru da sauran sojin da suka rasu

Mutum 2 sun fita da kumbo daga jirgin Janar Attahiru: Menene gaskiyar al'amarin?
Mutum 2 sun fita da kumbo daga jirgin Janar Attahiru: Menene gaskiyar al'amarin?
Asali: UGC

Hukunci

Wallafar da a halin yanzu aka gogeta karya ce. An yi ta ne dogaro da wani bidiyo dake yanar gizo tun 2018.

Cikakken bayani

A ranar Litinin, 21 ga watan Mayun 2021, shugaban sojin kasa na Najeriya, Ibrahim Attahiru da wasu sojoji 10 da suka hada da matukan jirgin saman sun rasu a hatsarin da aka yi a jihar Kaduna.

Washegari, wani rahoto daga Daily Post ya watsu inda aka ce ganau ba jiyau ba ya sanar da yadda wasu mutum biyu suka tsira daga hatsarin ta hanyar amfani da kumbo.

Binciken da Legit.ng tayi ta gano cewa an wallafa rahoton ne bayan wani Nwachukwu John Owen mai amfani da @johnown99 ya wallafa a Twitter.

Karin bincike yasa an gano cewa jama'a sun dinga wallafa bidiyon a Twitter da Facebook. A bidiyon, wani mutum aka ga yana bada labarin yadda jirgin ya fadi. Yace mutum biyu sun tsira bayan sun yi amfani da kumbo wurin fita.

Tantancewa

A yayin duba YouTube, Legit.ng ta gano asalin bidiyon inda aka yanka, shi kuwa wannan mutumin dake maganar, ba maganar hatsarin jirgin sama na Kaduna yake ba.

Voice TV Nigeria ce ta wallafa bidiyon a YouTube kuma tun ranar 28 ga watan Satumban 2018 aka wallafa.

KU KARANTA: Da duminsa: An gano abinda ya kawo hatsarin jirgin marigayi Janar Attahiru a Kaduna

Mutum 2 sun fita da kumbo daga jirgin Janar Attahiru: Menene gaskiyar al'amarin?
Mutum 2 sun fita da kumbo daga jirgin Janar Attahiru: Menene gaskiyar al'amarin?. Hoto daga @ChannelsTV
Asali: Twitter

Karin bayani ya nuna cewa bidiyon na wani horarwa ne ake yi domin shagalin bikin ranar samun yancin kai na Najeriya da jiragen NAF a 2018.

An yi hatsarin ne a Abuja a ranar 28 ga watan Satumban 2018. Mai magana da yawun rundunar sojin saman Najeriya, Ibikunle Daramola ya tabbatar da hakan a wata wallafa da yayi a Twitter.

A karshe, rahoton dake bayyana cewa mutum biyu sun fita daga jirgin saman da yayi hatsari da Attahiru da sauran sojoji 10 karya ne.

A wani labari na daban, Gawar Janar Ibrahim Attahiru, marigayi shugaban sojin kasa da sauran sojojin da suka rasu sakamakon hatsarin jirgin sama a ranar Juma'a an daukesu daga Kaduna zuwa Abuja.

Mamatan sun rasa rayukansu ne sakamakon hatsarin da suka yi da yammacin ranar Juma'a a Kaduna, Daily Trust ta ruwaito.

An kwashe gawawwakinsu daga inda suka yi hatsarin zuwa asibitin sojoji na 44 dake Kaduna daga nan aka mayar dasu Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: