Yadda na tsallake hatsarin jirgin sama da ya kashe Attahiru, Dan majalisar tarayya

Yadda na tsallake hatsarin jirgin sama da ya kashe Attahiru, Dan majalisar tarayya

- Abdulrazaq Namdaz dan majalisar wakilan Najeriya yace kiris ya rage ya bi jirginsu Attahiru zuwa Kaduna

- Ya sanar da yadda aka gayyace yayen sojojin da za'ayi a Zaria jihar Kaduna amma aiki ya tsare shi a Abuja

- Namdaz ya bayyana jimamin shi da kidimewar da yayi bayan jina labarin hatsarin jirgin saman da ya ritsa da COAS

Dan majalisar wakilai, Abdulrazaq Namdaz, ya bada labarin yadda ya kusa shiga jirgin saman da yayi hatsari har ya kashe shugaban sojin kasa, Ibrahim Attahiru da wasu jami'ai 10.

Namdaz wanda ke shugabantar kwamitin al'amuran sojin kasa ya sanar da hakan a wata tattaunawa da yayi da Channels TV a ranar Lahadi, 23 ga watan Mayu.

Dan majalisar yace an gayyaceshi domin halartar yayen sojoji da za a yi a Zaria, jihar Kaduna. Ya ce da zai je kuwa babu shakka jirgin su Attahiru zai bi.

KU KARANTA: Da duminsa: An gano abinda ya kawo hatsarin jirgin marigayi Janar Attahiru a Kaduna

Yadda na tsallake hatsarin jirgin sama da ya kashe Attahiru, Dan majalisar tarayya
Yadda na tsallake hatsarin jirgin sama da ya kashe Attahiru, Dan majalisar tarayya. Hoto daga @ChannelsTV
Asali: Twitter

Namdaz yace duk da gayyatarsa da aka yi, ba zai samu damar zuwa ba saboda wani aikin kwamitinsa na musamman da yake yi.

Dan majalisar yace: "Ko kafin faduwar jirgin, ya kamata in bi su saboda an gayyaceni yaye sojojin da za a yi a Zaria, jihar Kaduna.

"Dama a gaskiya mun saba bin su, idan ba don aikin kwamiti na musamman da nake ba wanda kakakin majalisa ya bani da tare da ni zamu yi hatsarin nan."

Namdaz yace ya matukar girgiza da labarin mutuwar Attahiru kuma ya kwatanta ranar da hatsarin ya auku da bakar rana.

Dan majalisar yace Attahiru ya bayyana iyawarsa da kuma yuwuwar kawo karshen ta'addancin Boko Haram a Najeriya.

KU KARANTA: Da duminsa: Gawar Janar Attahiru da sojoji 6 ta isa Abuja daga Kaduna

Dan majalisar ya koka da alamun rashin kyan jiragen saman Najeriya. Ya kwatanta lamarin da abun takaici yadda kasar ta fuskanci matsalar jiragen sama uku a cikin wata biyu.

Namdaz yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta shawo kan wannan matsalar gudun cigaba da rasa rayuka.

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin sauke tutoci domin karrama marigayi Ibrahim Attahiru, shugaban sojin kasa da sauran sojoji 10 da suka rasa rayukansu yayin hatsarin jirgin sama na Kaduna.

Sojojin 11 suna cikin jirgin saman sojin Najeriya yayin da yayi hatsari kusa da filin sauka da tashin jiragen sama na farar hula dake Kaduna a ranar Juma'a.

An shirya cewa Attahiru zai halarci taron yaye kananan sojoji a Kaduna a ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel