2006: Yadda hatsarin jirgin sama ya ritsa da sojoji masu mukamin janar 10 a Binuwai

2006: Yadda hatsarin jirgin sama ya ritsa da sojoji masu mukamin janar 10 a Binuwai

- A watan Satumban 2006 ne wani jirgin sojin Najeriya yayi hatsari a jihar Benue inda aka rasa sojoji 13

- Daga cikin sojojin da suka tunkari jihar Cross Rivers, akwai masu mukamin Janar-Janar har guda 10 duk suka rasu

- Ba kamar na Kaduna ba, an samu wasu sojoji masu mukamin Kanal har uku da suka rayu bayan hatsarin

A watan Satumban 2006, sojojin Najeriya da suka hada da janarori 10, laftanal kanal daya da wasu biyu sun rasu sakamakon hatsarin da Dornier 228-212 ya tafka a jihar Binuwai.

Sojojin na kan hanyarsu ta zuwa Obudu Cattle Ranch dake jihar Cross River, jaridar The Cable ta ruwaito.

Janarorin 10 da laftanal kanal din suna daga cikin kwamitin fadar shugaban kasa da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kafa domin gyaran rundunar sojin.

KU KARANTA: Buhari ya fada jimami, ya nuna damuwarsa tare da ta'aziyyar Janar Attahiru

2006: Yadda hatsarin jirgin sama ya ritsa da sojoji masu mukamin janar 10 a Binuwai
2006: Yadda hatsarin jirgin sama ya ritsa da sojoji masu mukamin janar 10 a Binuwai. Hoto daga @TheCableng
Asali: Twitter

Obasanjo wanda a lokacin yake kasar Singapore domin halartar taron shekara na IMF da bankin duniya, ya katse tafiyarsa inda ya gaggauta dawowa Najeriya. Daga bisani tsohon shugaban kasan ya bada hutun kwanaki uku a dukkan kasar domin zaman makoki.

Ba kamar hatsarin Beechcraft na Kaduna ba, a wannan sojoji uku masu mukamin kanal sun rayu.

A.N. Bamali, J.O. Adesunloye, J.O. Agboola, P.M. Haruna, J.T.U. Ahmedu, S.O. Otubu, B. Duniya da S.M. Lemu da dukkan manjo janar dake jirgin sun ce ga garinku bayan hatsarin.

Also, Y.J. Braimah da M.B. Bawa — dukkansu masu mukamin birgdiya janar — tare da E.O. Adekunle da O. Balogun, wing Kwamanda, duk sun rasu a hatsarin.

N.A. Mohammed, soja mai mukamin laftanal kanal ya rasu a hatsarin.

O.C. Ajunwa, N.I. Angbazo da A.L. Dusu sojoji ne masu mukamin kanal da suka gwabza hatsarin amma suka rayu.

KU KARANTA: Rundunar sojin Najeriya ta sanar da ranar birne Janar Attahiru da sauran sojin da suka rasu

A wani labari na daban, hedkwatar tsaro ta kasa ta bayyana dalilin da ya kawo tarwatsewar jirgin sama wanda yayi sanadiyyar mutuwar shugaban sojojin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da wasu sojoji 10 a ranar Juma'a, 21 ga watan Mayun 2021.

Kamar yadda Onyema Nwachukwu, mai magana da yawun hedkwatar tsaro ya sanar, duk da ana cigaba da binciken sanadin lamarin, hatsarin ya auku ne bayan jirgin ya sauka a filin sauka da tashin jiragen saman na Kaduna.

Duk da da dai, Nwacukwu ta shafin hedkwatar tsaron na Twitter, ya bayyana cewa Janar Lucky Irabor, shugaban ma'aikatan tsaro ya bada umarnin binciken lamarin da ya kawo mummunan hatsarin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel