An Sallami Malaman Makarantun Frimare 20 Daga Aiki a Niger

An Sallami Malaman Makarantun Frimare 20 Daga Aiki a Niger

- Hukumar SUBEB na jihar Niger ta sallami malaman makarantun frimare 20 daga aiki

- Hakan ne zuwa ne bayan samun wasunsu da shaidar karatu na bogi da rashin zuwa aiki

- Hukumar ta ce wannan wani mataki ne na yin fatali da bara-gurbi daga cikin malamai kuma za ta cigaba da tantance su

Hukumar kula da makarantun frimare ta jiha, SUBEB, ta jihar Niger ta kori malaman makarantun frimare 20 a sassan jihar daga aiki saboda satifiket ɗin bogi da rashin zuwa aiki.

A cewar kamfanin dillancin labarai, NAN, an sanar da korar su ne cikin wata sanarwa da Idris Kolo, kakakin SUBEB, ya fitar a ranar Litinin kamar yadda The Cable ta ruwaito.

An Sallami Malaman Makarantun Frimare 20 Daga Aiki a Niger
An Sallami Malaman Makarantun Frimare 20 Daga Aiki a Niger. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan Bindiga Sun Sace Matar Shugaban Matasa na APC a Kofar Gidanta

Idris Adamu, Shugaban SUBEB na Niger, ya ce an kori malamai huɗu daga Gbako, sai uku-uku daga Bida da Lapai.

Ya kuma ce an sallami biyu daga aiki a ƙananan hukumomin Agaie, Katcha da Lavun yayin da aka sallami mutum ɗai-ɗai a ƙananan hukumomin Mashegu, Munya da Shiroro. Ya kuma ce an kori malami ɗaya a Kontagora saboda rashin zuwa aiki.

"Hukumar ta yanke shawarar korar dukkan malaman da ba su cancanta ba a makarantun frimare a matsayin wani mataki na inganta koyarwa da karantarwa a makarantun frimare na jihar," in ji shi.

KU KARANTA: Masu Zanga-Zanga Sun Tare Hanyar Abuja-Kaduna Kan Sace Mutum 30 Da Yan Bindiga Suka Yi

Shugaban na SUBEB ya ce hukumar tana mataki na farko na tantance ma'aikata ne kuma za ta cigaba da fatattakar ɓara-gurbi daga cikin ma'aikatan.

A wani labarin daban, kun ji cewa a kalla mutane biyu ne suka rasu sakamakon fashewar bututun iskar gas a cikin harabar Dakin Karatu na tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL) da ke Abeokuta jihar Ogun a safiyar ranar Alhamis, rahoton Daily Trust.

Dakin karatun ba shi da nisa da wani otel inda fashewar gas ya kashe mutane hudu kwanaki biyu da suka gabata.

Otel din mai suna Conference Hotel inda abin bakin cikin ya faru mallakin tsohon gwamnan jihar Ogun Gbenga Daniel ne.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel