Kada Mutuwar Janar Attajiru Ta Kashe Muku Kwarin Gwiwa, IGP Ga Sojojin Najeriya
- Mukaddashin Sufeto Janar na 'yan sanda ya jajantawa rundunar sojin Najeriya bisa babban rashin COAS
- IGP din ya bayyana jimaminsa tare da shawartar jaruman sojojin Najeriya cewa kada kwarin gwiwar ta ragu
- Ya siffanta marigayin a matsayin jarumi mai aiki tukuru don tabbatar da zaman lafiya a fadin Najeriya
Mukaddashin Sufeto-Janar na 'yan sanda, Usman Baba, ya bukaci sojojin Najeriya da ke yaki da tayar da kayar baya da sauran laifuka a fadin kasar nan da kar su bari mutuwar Shugaban hafsan sojoji, Laftanal-Janar Ibrahim Attahiru ta rage musu kwarin gwiwa.
Baba, yayin da yake juyayin marigayi COAS da sauran hafsoshin soja da matukan jirgin da suka mutu a wani mummunan hadarin jirgi a Kaduna yayin da suke kan aikin kasa a ranar Juma’a, ya bayyana lamarin a matsayin ‘’abin bakin ciki." Daily Trust ta ruwaito.
Ofishin Binciken Hadurra na Najeriya (AIB) a ranar Asabar, an ba ta ikon jagorantar bincike kan musabbabin hadarin jirgin saman na Air Force Beechcraft 350 da ya kashe Shugaban Hafsun Sojin, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru Vanguard ta ruwaito.
KU KARANTA: Yadda ISWAP Ta Yi Amfani da Mata da Yara Wajen Hallaka Shekau
A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar, Frank Mba, IGP ya bayyana marigayi COAS a matsayin:
“Kwararren masanin dabarun soja, aboki da ba za a iya kimanta shi ba kuma babban abokin tafiya a ci gaba da yaki da tayar da kayar baya da sauran kalubalen tsaro a kasar."
Sanarwar ta ce, “IGP na rokon mambobin sojojin Najeriya, musamman jami’ai da jarumai na Sojojin Najeriya, da kada su bari wannan abin bakin ciki ya lalata musu kwarin gwiwarsu."
IGP ya bukace su da "Su ci gaba da mai da hankali kan neman hadin kan dawo da doka da oda a cikin kasar kamar yadda hakan zai kasance mafi dacewa da girmamawa da za mu iya yi wa marigayi Janar tare da sauran jaruman da suka mutu.''
Baba ya bayyana cewa lamarin ya fi matukar ciwon gaske ganin cewa jami'ai masu matukar biyayya, masu kwazo da kwararru suma sun mutu a hadarin jirgin.
"Wannan kari ne ga gaskiyar cewa ya bar kasar da yake matukar kauna kuma a wani lokacin da kwarewarsa da hidimarsa suke da matukar muhimmanci ga zaman lafiyarmu," in ji shi.
KU KARANTA: Da Duminsa: Ba Za Mu Kara Farashin Man Fetur Yanzu Ba, Gwamnatin Buhari
A wani labarin, Iyalai, 'yan uwa da masoyan marigayi shugaban sojin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da sauran sojojin da suka rasu a hatsarin jirgin sama na Kaduna a ranar Juma'a sun je jana'iza tare da taya makokin mutuwar da aka yi har zuwa makabartar sojoji.
Hatsarin jirgin saman wanda ya lakume rayukan dakarun sojin, ya auku ne saboda yanayin gari mara kyau bayan jirgin yayi yunkurin sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na farar hula dake Kaduna.
Matar shugaban sojin Najeriya da 'yan uwansa, masoya da abokan arziki sun kasa boye tashin hankalinsu yayin da ake birne dakarun, Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng