Muhimman abubuwa 5 da baku sani ba game da kungiyar ISWAP

Muhimman abubuwa 5 da baku sani ba game da kungiyar ISWAP

- Rahotanni kan mutuwar shugaban kungiyar Boko Haram wanda kungiyar ISWAP tayi sanadi ya baiwa jama'a mamaki

- Kungiyar ISWAP ta rabe daga Boko Haram tun a shekarar 2016 inda aka baiwa Abu al-Barnawai shugabancinta

- Kungiyar jihadin tana da tsarika daban-daban, yankinta, kafuwarta, mulki da kuma yanayin ta'addancin da take aiwatarwa

Rahotanni kan mutuwar shugaban kungiyar ta'addanci ta Boko Haram, Abubakar Shekau yana ta yaduwa inda ake alakanta ta da kutse da miyagun mayakan ISWAP suka yi a dajin Sambisa.

Ga jerin abubuwa biyar da baku sani ba game da 'yan ta'addan ISWAP:

1. Samuwarta

ISWAP ta samo asali ne bayan rabuwar wani bangaren Boko Haram da Shekau ke jagoranta. Rabewar ta auku ne a 2016 bayan sun koma sun yi mubaya'a ga kungiyar ta'addanci ta yammacin Afrika.

KU KARANTA: Nan babu dadewa zaman lafiya zai dawo Najeriya, Ministan tsaro

Muhimman abubuwa 5 da baku sani ba game da kungiyar ISWAP
Muhimman abubuwa 5 da baku sani ba game da kungiyar ISWAP. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Birane 5 dake karkashin kasa, wurin da suke da labaransu masu cike da al'ajabi

2. Shugabanci

An nada Abu al-Barnawi a matsayin shugaban ISWAP na farko a 2016 kuma wannan na daga cikin abinda yasa Shekau yace ba zai zauna karkashin kowanne shugaba ba.

Kamar yadda kwararru suka ce, al-Barnawi dan asalin wanda ya kirkiro Boko Haram ne, Mohammed Yusuf kuma ya taba zama mai magana da yawun Boko Haram karkashin Shekau.

A watan Maris na 2019, wani mai suna Ba Idrisa ya zama shugaban ISWAP kuma an ragewa Al-Barnawi matsayi inda ya zama mamba a kwamitin Shura.

3. Iyakokinta

ISWAP ta kafa iyakokinta daga gaba zuwa tsibirin tafkin Chadi da kuma arewa maso gabas na Najeriya. Kungiyar ta kware wurin tada yaki a wadannan yankunan.

ISWAP na cigaba da kafa rassanta zuwa yankunan farar hula a kasashen Kamaru da Nijar.

4. Ta'addanci

A matsayinta na kungiyar da ta rabe daga wata, ISWAP ta cigaba da kaiwa Boko Haram farmaki wanda hakan ya dinga zama sanadin mutuwar jama'a da dama daga kungiyoyin biyu.

Kungiyar ta cigaba da tabbatar da yaki a yankin arewa maso gabas na Najeriya. A watan Mayun shekarar da ta gabata, dakarun Najeriya sun halaka mayakan ISWAP 78.

5. Tsarin mulki

Duk da ISWAP ta rungumi salon tarzoma da saka karfi wurin ayyukanta, kungiyar jihadin ta mamaye garuruwan yankin da kuma na tsibirin Chadi, inda ta tsaya tsakanin mulki da goyon baya.

ISWAP na mulkar mazauna yankin tafkin Chadi, inda ta zama tamkar gwamnati tana samar da tsarin kiwon lafiya, satar shanu, haka rijiyoyi da kuma haraji.

A wani labari na daban, Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram ya sheka lahira yayin wata arangama da mayakan kungiyar ta'addanci ta ISWAP kamar yadda rahotanni suka bayyana.

A yayin bayyana wani bayanin sirri, Daily Trust ta ruwaito yadda shugaban kungiyar miyagun ta Boko Haram ya rasa rayuwarsa bayan musayar wuta da mayakan ISWAP.

A wani rahoton yadda lamarin ya faru, HumAngle ta ruwaito cewa wasu kwamandojin ISWAP sun rasa rayukansu tare da Shekau.

Hakazalika, jaridar tace a ranar Laraba ne mayakan ISWAP sun kutsa dajin Sambisa a motocin yaki, yankin da marigayi Shekau ya mamaye kuma suka tirsasa Shekau da ya mika kansa bayan an fi karfin dakarunsa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel