Dalla-dalla: Yadda Shekau ya sheka lahira tare da wasu kwamandojin ISWAP

Dalla-dalla: Yadda Shekau ya sheka lahira tare da wasu kwamandojin ISWAP

- An gano cewa mayakan ISWAP sun mamaye dajin Sambisa inda suka fi karfin dakarun Shekau tun a ranar Laraba

- Shugabannin ISWAP sun bukaci Shekau da ya mika wuya sannan dakarunsa su yi mubaya'a garesu

- Sai dai Shekau nuna tamkar ya amince, sannan ya tashi bam dake jikinsa yayin da suke ganawar sa'o'i da kwamandojin ISWAP

Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram ya sheka lahira yayin wata arangama da mayakan kungiyar ta'addanci ta ISWAP kamar yadda rahotanni suka bayyana.

A yayin bayyana wani bayanin sirri, Daily Trust ta ruwaito yadda shugaban kungiyar miyagun ta Boko Haram ya rasa rayuwarsa bayan musayar wuta da mayakan ISWAP.

KU KARANTA: El-Rufai: Duk wadanda suka rufe kasuwanci da sunan yajin aiki zasu dandana kudarsu

Dalla-dalla: Yadda Shekau ya sheka lahira tare da wasu kwamandojin ISWAP
Dalla-dalla: Yadda Shekau ya sheka lahira tare da wasu kwamandojin ISWAP. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: An sheke mutum 1, wasu sun bace yayin da 'yan bindiga suka kai farmaki Katsina

A wani rahoton yadda lamarin ya faru, HumAngle ta ruwaito cewa wasu kwamandojin ISWAP sun rasa rayukansu tare da Shekau.

Hakazalika, jaridar tace a ranar Laraba ne mayakan ISWAP sun kutsa dajin Sambisa a motocin yaki, yankin da marigayi Shekau ya mamaye kuma suka tirsasa Shekau da ya mika kansa bayan an fi karfin dakarunsa.

An gano cewa sun bukaci Shekau da yayi mubaya'a amma yace gara ya kashe kansa da yayi hakan, lamarin kuwa da ya faru.

"Bayan fin karfin dakarunsa, Shekau ya mika wuya kuma sun shiga ganawa da mayakan ISWAP na sa'o'i masu yawa. A nan ne suka bukacesa da ya mika wuya sannan ya kira mayakansa da su yi mubaya'a ga hukumar ISWAP. Sun yi tsammanin Shekau zai aminta da hakan.

“Majiyoyi daga cikin 'yan ta'addan tace dama Shekau na sanye da rigar bam wacce a take ya tashi da kowa dake wurin wannan sasancin. Har a halin yanzu ba a gano yawan shugabannin ISWAP din da wannan al'amarin ya rutsa dasu ba," HumAngle tace a rahotonta.

A wani labari na daban, ministan tsaro, Bashir Magashi, ya ce nan babu dadewa za a shawo kan matsalar rashin tsaro kuma Najeriya zata samu zaman lafiya.

Ministan wanda ya samu wakilcin Lucky Irabor, shugaban ma'aikatan tsaro, ya sanar da hakan ne a wani taro kashi na 57 da aka yi a NAF Makurdi, babban birnin jihar Binuwai.

Ana samun jerin hare-hare a fadin kasar nan wanda ke kawo mutuwar jama'a, garkuwa da mutane da kuma kona gine-ginen gwamnati, The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng