Rahoto: Jerin Sunayen Kwamandojin Boko Haram da ISWAP ta Damke

Rahoto: Jerin Sunayen Kwamandojin Boko Haram da ISWAP ta Damke

- Kungiyar ISWAP ta fitar da jerin sunayen 'yan ta'addan Boko Haram da suka kame a harin da suka kai

- Sun jero sunayen kwamandojin kungiyar Boko Haram da ta cafke bayan artabu da suka yi tsakaninsu

- An ruwaito cewa, shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya mutu a yayin bata-kashin

Kungiyar 'yan ta'adda ta ISWAP karkashin sabon jagorancin Abu-Musad Albarnawy ta karbe dukkan yankuna da ke karkashin ikon marigayi Abubakar Shekau a wani babban hari da aka kai wa tsohon shugaban na Boko Haram.

Wasu majiyoyi masana game da kungiyoyin ‘yan ta’addan sun ce bangaren na ISWAP ya kame manyan kwamandoji 30 masu biyayya ga marigayi shugaban Boko Haram, Vanguard ta ruwaito.

KU KARANTA: An Kuma: 'Yan Ta'adda Cikin Kakin Soja Sun Kashe Jami'in Dan Sanda a Jihar Imo

Rahoto: Jerin Sunayen Kwamandojin Boko Haram da ISWAP ta Damke
Rahoto: Jerin Sunayen Kwamandojin Boko Haram da ISWAP ta Damke Hoto: ifm923.com
Asali: UGC

Wadanda aka kame sun hada da:

1. Abdul Bash, Kwamandan Parisu

2. Abu Mujaheed, Kwamandan Sabil Huda

3. Mala Ali, Kwamandan Farisu

4. Amir Hassana, Kwamandan Garin Dambe

5. Malam Bako, Kwamandan Hizba

6. Amir Halid, Kwamandan Njimiya Falluja, Kwamandan Garin

7. Mala Abu- Fatima, Kwamandan Gwashke

8. Kaka BK, Kwamandan Garin Abu Asmau

9. Alai Bukar, Kwamandan Mina Ngawri

10. Abu-Ubaida, Kwamandan Jungle Gabra a Pulka

11. Amir Abdulrahman, Kwamandan Gobara

12. Abu Muhammad, Kwamandan Alava

13. Ali Shara, Kwamandan Yuwe Hanyan Bama

14. Amir Huzayfa, Kwamandan Yuwe Hanyan Maraba

15. Abubakar Sarki, Kwamandan Yuwe Hanyan Konduga

16. Ibn Abbas, Kwamanda Barin Bulla Yaga

17. Ali Ngule, Kwamandan Madara Kwamanda

18. Ummati Mai Shayi, Kwamandan Madara Dutsen

19. Mala Musa Abuja, Babban Mai Kera Bam

20. Mallam Bana Sharra, Babban Alkali a bangaren Shekau, wanda ke Garin Mala Hassan

21. Baba Dr. Konduga, Babban Likitan Lafiya

22. Alava Road, Ma’azu Dan Lokodisa, babban jami’in gidan yari

23. Alai Abba, mai kula da Mata da yara

24. Mala Musa, Babban Jami'in Injiniya, wanda ke Parisu

25. Abu Zaid, Babban mai hada bam, wanda ke Parisu

26. Abu Aisha shugaban ayyuka na musamman

27.Amir Okasha, mai lura da lokacin bam,

28. Farisu da Amir Awana

29. Da sauran manyan 'yan ta'adda.

Sai dai, rundunar sojin Najeriya ta ce bata samu tabbacin cewa shugaban kungiyar ta Boko Haram din ya mutu ba, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Mutuwar Shekau Ya Isa Darasi Ga Nnamdi Kanu da Sunday Igboho, Adama Garba

A wani labarin, Wasu da ake zargin 'yan ISWAP ne a ranar Laraba sun kashe shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, yayin wani kazamin fada a maboyar su ta Dajin Sambisa. In ji wata majiya da ba a tabbatar ba, Vanguard ta ruwaito.

Gandun dajin Sambisa yana da iyaka da kananan hukumomin Konduga, Bama, Gwoza Askira Uba, Hawul, Kaga da Biu a kananan hukumomin Borno, tare da wasu yankuna na Gujuba, Buni Yadi, Goniri a Yobe da Madagali a jihar Adamawa.

Wasu majiyoyi sun ce daruruwan mayakan ISWAP sun mamaye Sambisa da motoci dauke da manyan bindigogi da ke farautar Shekau wanda shi ne shugaban kungiyar Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel