Gwamna El-Rufai ya yi wa Gwamnoni kaca-kaca, NGF ta bukaci a koma saida litar fetur N408
- A wajen taron NGF, Nasir El-Rufai ya zargi gwamnoni da juya masa baya
- Gwamnan Kaduna yana ganin NGF ta bar sa shi kadai ya na fada da NLC
- Kwamitin NGF ya bada shawarar a tsaida farashin litar fetur a kan N408
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya zargi abokan aikinsa da watsi da shi a lokacin da yake tsakiyar rigima da kungiyar kwadago ta kasa.
Jaridar Punch ta ce Nasir El-Rufai ya yi wannan bayani ne a wajen taron kungiyar gwamnonin Najeriya na NGF wanda aka yi ta kafar yanar gizo a jiya.
A wajen wannan taro, kwamitin da NGF ta kafa domin ya tsaida farashin man fetur ya bada shawarar a rika saida litar mai tsakanin N380 da N408.5.
KU KARANTA: Ba za mu je Abuja mu zauna da NLC ba ... - El-Rufai
The Eagle ta ce kwamitin ya bukaci gwamnati ta cire tallafin man fetur. Kafin wannan kwamiti ya gabatar da rahotonsa ne, El-Rufai ya soki takwarorinsa.
Malam El-Rufai ya ce akwai wani gwamna da ya taimaka wa shugabannin kungiyar NLC da kudi domin ‘yan kwadago su kawo tashin-tashina a jihar Kaduna.
Ya ce: “Ni gwamna ne. Ina cikinku. Akalla abin da nake tunanin NGF za ta yi mani, shi ne ta mara mani baya 100-bisa-100. Sam ban ga wannan a jawabinku ba.”
“Ina fada maku gaskiya ne. Zan iya yin na ‘yan siyasa, in yi murmushi, in ce komai kalau, amma ba haka ba ne. Amma na saba yin fadana da kai na.” inji sa.
KU KARANTA: Wadanda su ka yi yajin-aiki za su dandana kudarsu - KDSG
Bayan sukar kungiyar ‘yan kwadagon, gwamnan na jihar Kaduna ya ce babu barazanar da ta zarce NLC a Najeriya, ya yi kira ga gwamnoni suyi maganinsu.
Gwamnan ya na ganin siyasa ce ta sa NLC ta shiga yajin-aiki a Kaduna domin akwai sauran jihohin da ke korar ma’aikata, kuma ba a biyan albashi da kyau.
A game da farashin fetur, gwamnan Kaduna ya ce gwamnati ta na asarar N70b-N210b a kowane wata saboda ana saida litar man fetur a kan N165 har yanzu.
Kwamitin na NGF ta bakin gwamna Nasir El-Rufai ya bada shawarar a saida man fetur a kan N408.5, idan ‘yan kwadago sun matsa, sai a bar farashin a N380.
A jiya aka ji Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sa labule da ‘Yan Kwankwasiyya da shugabannin PDP bayan rade-radin an samu barakar cikin gida a jihar Kano.
Da alama, jam’iyyar PDP za ta so a shawo kan duk wata matsala kafin a tunkari APC a 2023 a Kano.
Asali: Legit.ng