Da duminsa: Sojoji sun dira a Oshodin Legas, sun ragargaza ababen hawa masu yawa

Da duminsa: Sojoji sun dira a Oshodin Legas, sun ragargaza ababen hawa masu yawa

- An samu tashin hankali a jihar Legas bayan sojoji sun dira yankin Oshodi dake Legas domin daukan fansan kisan abokin aikinsu

- Wasu 'yan daba dake yankin sun kashe hafsin sojan saman Najeriya a yankin Oshodi, lamarin da ya tada hankula

- Wannan al'amarin ya matukar tada hankula saboda tarwatsa wasu ababen hawa da aka yi sannan mutane sun kasa samun hanyar barin wurin

Mazauna da masu wucewa yankina Oshodi sun tsaya cirko-cirko dake jihar Legas sakamakon mamaye yankin da sojoji suna yi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ana zargin sojojin sun tsinkayi yankin a safiyar Alhamis, 20 ga watan Mayu domin daukar fansan kisan wani hafsin sojan sama da aka yi.

KU KARANTA: Kudaden da aka wawure: FG ta samo sama da $700m a cikin shekaru 4, Malami

Da duminsa: Sojoji sun dira a Oshodin Legas, sun ragargaza ababen hawa masu yawa
Da duminsa: Sojoji sun dira a Oshodin Legas, sun ragargaza ababen hawa masu yawa. Hoto daga PIUS UTOMI EKPEI/AFP
Asali: Getty Images

KU KARANTA: El-Rufai: Duk wadanda suka rufe kasuwanci da sunan yajin aiki zasu dandana kudarsu

Legit.ng ta tattaro cewa ababen hawa, ballantana motocin haya duk an tarwatsa su tare da lalatasu yayin da fusatattun sojojin suka dinga cin zarafin jama'a.

An gano cewa wasu mazauna yankin da suka kama hanyar zuwa wurin aiki sun dakata saboda rikicin yayin da dalibai 'yan makaranta ke gudun dawowa gidajensu.

'Yan kasuwa dake sharar shagunansu sun gaggauwat barin yankin yayin da masu ababen hawa na haya suka bar ababen hawansu domin ceton rayukansu.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, Muyiwa Adejobi, yace yana jiran rahoton aukuwar lamarin daga ofishin 'yan sandan yankin, The Punch ta ruwaito.

A wani labari na daban, wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari garin Batsari, hedkwatar karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina inda suka kashe mutum daya tare da yin awon gaba da wasu masu yawa.

Wani mazaunin Batsari wanda ya zanta da Daily Trust a waya yace Alhaji Iliya Bakon-Zabo, wanda ya koma Batsari a shekaru shida da suka gabata ne aka kashe yayin harin.

Ya ce kusan mutum 27 ne suka bace duk da har yanzu ba za a ce ko 'yan bindigan ne suka tisa keyarsu ba.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel