Za a Ware Wa Masu Addinan Gargajiya Ranar Hutu Tamkar Sallah da Kirsimeti a Legas

Za a Ware Wa Masu Addinan Gargajiya Ranar Hutu Tamkar Sallah da Kirsimeti a Legas

- Gwamnatin jihar Legas tana aiki kan kudiri na bawa masu addinan gargajiya ranarsu ta hutu a kowanne shekara

- A halin yanzu akwai kudirin doka a majalisar dokokin jihar wadda ake sa ran za a amince da shi kuma gwamna zai saka hannu

- Kwamishinan al'adu na Legas ta ce addinin gargajiya al'adda ce ta mutanen jihar kuma addinin kakakin da iyaye kafin zuwa kiristanci da musulunci

Nan bada dadewa ba gwamnatin jihar Legas za ta ware wa masu addinan gargajiya ranakun hutunsu na musamman duk shekara domin suyi biki kamar ta Kirsimeti da Sallah, Daily Trust ta ruwaito.

Kwamishinan harkokin yawon bude ido, Mrs Uzamat Akinbile Yussuf da mai bawa gwamna shawara na musamman kan harkokin bude ido da al'addu, Mr Solomon Bonu ne suka bayyana hakan yayin bada rahoton ayyukansu na shekaru biyu da suka gabata.

Za a Ware Wa Masu Addinan Gargajiya Ranar Hutu Tamkar Sallah da Kirsimeti a Legas
Za a Ware Wa Masu Addinan Gargajiya Ranar Hutu Tamkar Sallah da Kirsimeti a Legas. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sarkin Kano Ya Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Jirgin Sama Ya Kusa Hatsari

A cewar Bonu, an halin yanzu kudirin dokar ware ranar hutu ta musamman domin masu addinan gargajiya yana gaban majalisar jihar; Ya bada tabbacin yan majalisar za su amince da shi kuma Gwamna Babajide Sanwo Olu zai saka hannu.

Idan an yi dokar, za a ware rana ta musamman na hutu domin biki na masu addinan gargajiya.

"A ranar, wadda akwai yiwuwar za ta kasance a Agusta, gwamnati za ta shirya shagulgila domin taya su murna inda dukkan masu bautan za su taru. Wannan al'adar mu ce, ita ce addinin farko kuma addinin kakaninmu kafin addininan kirista da musulunci su zo. Don haka, rana ce da za mu baje kolin al'adun mu," in ji shi.

KU KARANTA: Gini Ya Faɗowa Wani Mutum Yayinda Ya Ke Fitsari a Bayan Gidansa

Ya kuma kara da cewa dokar za ta tantance abubuwan da masu addinan za su rika yi domin kada su wuce gona da iri a kuma mayar da shi hanyar jawo hankalin masu yawon bude ido a Legas.

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Raya Birnin Tarayya Abuja, FCTA, ta rushe wani tashar tasi a NICON Junction, Maitama, Abuja, kan zargin mayar da tashar matattarar yan kwaya da bata gari, Daily Trust ta ruwaito.

Direktan (FCTA), sashin tsaro, Adamu Gwari, wanda ya yi magana yayin rushe tashar ya ce tashar barazanar tsaro ne sannan barazana ne ga muhallin mutanen da ke zaune a birnin. An Rushe Tashar Motar Saboda Ta Zama 'Matattarar Ƴan Ƙwaya' a Abuja.

Ya kuma ce rushe tashar mataki ne da aka dauka duba da irin kallubalen tsaron da ake fuskanta a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: