Bahaushe ya ceci rayuwata, da tun tuni Gwamnan Imo ya sa an bindige ni – Okorocha
- Rochas Okorocha ya koka game da alakarsa da Gwamna mai-ci Hope Uzodinma
- Tsohon Gwamnan jihar Imo ya ce Uzodinma ya dauki karon-tsana ya daura masa
- Okorocha yace kwanakin baya sai da gwamnatin Uzodinma ta nemi ta hallaka shi
Tsohon gwaamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya yi hira da jaridar Channels TV, inda ya bayyana irin alakar da ke tsakaninsa da Hope Uzodinma.
Sanata Rochas Okorocha ya koka a kan yadda gwamna mai-ci Hope Uzodinma ya dauki karon-tsana ya daura masa, yace ya rasa abin da ya jawo kiyayyar.
Rochas Okorocha wanda ya yi mulkin jihar Imo tsakanin shekarar 2011 da 2019 ya bayyana yadda gwamnatin Sanata Hope Uzodinma ta ke hantararsa da iyalinsa.
KU KARANTA: Har yau an gaza kammala shari’ar EFCC da Diezani Madueke
Okorocha ya yi wannan bayani ne a lokacin da aka yi hira da shi a shirin Sunday Politics a ranar Lahadi.
Sanatan na jihar Imo ta yamma ya ce da farko ya yi tunanin wasu ne suke zuga gwamnan, amma daga baya ya fahimci cewa haka kurum ya kudiri yaki da shi.
Sanata Okorocha ya sha alwashin ba zai maida wa Sanata Hope Uzodinma martani ba, ya ce a matsayinsa na uba, wannan ne zai sa a zauna lafiya a jihar Imo.
Jigon na jam’iyyar APC a kudu maso gabashin Najeriya ya gargadi gwamna Uzodinma da cewa komai ya yi farko zai yi karshe, ya ce wata rana zai bar kan mulki.
KU KARANTA: Rashin kunya Hadiza Bala Usman ta rika yi wa manya - Sanata
A cewar Okorocha, kwanakin baya sai da gwamnan Imo ya nemi ya hallaka shi, ya ce an aiko wasu tsageru su harbe shi, amma Ubangiji ya nufa da sauran kwana.
Sanatan ya ce lokacin da ya je jin abin da ya sa aka rufe wani otel da mai dakinsa ta mallaka, sai ‘yan sanda su ka yi ram da shi, sannan ‘yan bindiga su ka auko masa.
A nan ne wani Bahaushen ‘dan sanda ya yi maza ya fadawa Okorocha ya shiga cikin mota, wannan ya ceci rayuwarsa, ya ce ba don haka ba da tuni an harbe shi.
Dazu kun ji cewa a lokacin da gwamnatin Goodluck Jonathan take mulki tsakanin Mayun 2010 zuwa Mayun 2015, Nasir El-Rufai ya na cikin manyan ‘yan adawarta.
Gwamnan na yau, ya soki karin kudin man fetur da Goodluck Jonathan ya yi. Sai kuma ga shi a yau, Gwamnan na Kaduna ya na yaki da masu y masa zanga-zanga.
Asali: Legit.ng