Shugaban PDP zai kai karar ‘Dan Jam’iyya kotu bayan ya zarge shi da lakume Biliyan 10

Shugaban PDP zai kai karar ‘Dan Jam’iyya kotu bayan ya zarge shi da lakume Biliyan 10

- Prince Uche Secondus ya na barazanar shigar da karar Mr. Kassim Afegbua

- Shugaban PDP ya na zargin Kassim Afegbua da yi masa sharrin satar kudi

- Lauyoyin Secondus sun bukaci Afegbua ya bada hakuri, sannan ya biya N1bn

Bayan zargin da aka jefe shi da shi a makon da ya gabata na cewa akwai hannunsa a badakalar cin Naira biliyan 10, Prince Uche Secondus ya kai maganar kotu.

A ranar Alhamis, shugaban PDP na kasa, Prince Uche Secondus, ya kai karar Kassim Afegbua, ya na neman kotu ta tursasa shi ya janye zargin da ya jefe shi da shi.

Bayan janye kalaman da ya yi, shugaban PDP na kasa ya nemi Kassim Afegbua ya biya kudi har Naira biliyan 1 a sakamakon bata masa suna da ci masa zarafi da ya yi.

KU KARANTA: Fasto Mbaka ya bukaci Majalisa su taru su sauke Shugaba Buhari

Uche Secondus ya kai kara ne ta hannun lauyansa, Emeka Etiaba, wanda ya ba Afegbua wa’adin kwana biyu ya janye maganarsa ko kuma su hadu a gaban kuliya.

Kamfanin lauyoyin Emeka Etiaba Chambers da suka wakilci shugaban PDP sun ce idan Afegbua bai biya wanda su ke wakilta Naira Biliyan 1 ba, za su yi shari’a.

Lauyan Emeka Etiaba Chambers watau Kayode Ajulo ya fada wa jigon na PDP wannan. Lauyoyin su ka ce ikirarin Afegbua ya bata sunan Mista Uche Secondus a gari.

Kafin yanzu Afegbua ya rike kujerar kwamishinan yada labarai a jihar Edo a gwamnatin PDP.

KU KARANTA: Kudirin da zai kirkiro kujeru 3 a kowace Jiha ya na samun karbuwa

Shugaban PDP zai kai karar ‘Dan Jam’iyya kotu bayan ya zarge shi da lakume Biliyan 10
Shugaban PDP na kasa
Asali: Twitter

A takardar da ka aika wa tsohon kwamishinan, an tuna masa Secondus ya rike mukamai a NAICOM, NIMC da NRC ba tare da an zarge shi da yin ba daidai ba.

“Abin da ka fada wanda ka san karya ne, ya jawo wa wanda mu ke wakilta abin surutu, an jefa shakku game daaaaaaaaaaaaaa matsayinsa na zama mutum mai daraja a al’umma.”

Lauyoyin sun bukaci Afebua ya koma gidajen jaridun da ya soma yada wannan ‘karya’, ya nemi afuwa.

A baya kun jiya yadda wata sabuwar rigima ta ke neman kunno kai a jam’iyyar hamayya ta PDP inda ake tuhumar shugabannin jam’iyya da zargin cin makudan kudi.

Prince Kassim Afegbua ya na zargin shugaban jam’iyyar PDP da salwantar da Naira biliyan 10, amma bai bada wasu hujjoji da za su iya gaskata ikirarin da ya ke yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel