Boko Haram na amfani da damar annobar korona wajen dawowa Najeriya, Buhari

Boko Haram na amfani da damar annobar korona wajen dawowa Najeriya, Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce Boko Haram na amfani da damar annobar korona wajen dawo da hare-hare Najeriya

- Buhari ya bayyana hakan ne a wajen taron koli na kasashen Afrika da ke gudana a kasar Faransa

- Ya yi kira ga kulla alaka tsakanin Faransa da Najeriya domin yakar ta'addanci wanda dukkan kasashen ke fama da shi

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce maharan Boko Haram sun yi amfani da damar wannan cuta ta coronavirus don kaddamar da hare-hare a Najeriya, jaridar The Cable ta ruwaito.

Buhari ya bayyana hakan ne a wata kasida da aka wallafa a ranar Talata, 18 ga watan Mayu a mujallar mako-mako ta Faransa.

A ranar Lahadi ne, shugaban Najeriyan ya bar Abuja zuwa kasar Faransa gabanin taron koli kan harkokin kudi na kasashen Afirka da ke fama da cutar coronavirus.

Boko Haram na amfani da damar annobar korona wajen dawowa Najeriya, Buhari
Boko Haram na amfani da damar annobar korona wajen dawowa Najeriya, Buhari Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Da dumi: Shahararren gwamnan Najeriya ya rushe majalisarsa gaba daya, abun ya shafi SSG da Shugaban ma’aikata

Tattaunawar taron wanda aka gudanar ranar Talata, ya ta'allaka ne game da barazanar tsaro a yankin Sahel da Tafkin Chadi, canjin yanayi, alakar tattalin arziki, alakar siyasa, da lafiya.

Jaridar Daily Trust ta kuma ruwaito cewa Shugaban kasar ya jaddada bukatar Najeriya da Faransa su zurfafa hadin gwiwar yaki da ta'addanci don shawo kan matsalar, musamman bayan kisan Marigayi Shugaban Chadi.

A cikin jawabin, Buhari ya ce Najeriya da Faransa suna da abokin gaba daya kamar COVID-19, wanda shine ta'addanci, ya kara da cewa kasashen biyu na bukatar hadin kai don magance lamarin yadda ya kamata.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Gwamna Abiodun ya sallami hadiminsa da aka kama a Amurka kan zambar $350,000

Shugaba Buhari, wanda ya mayar da hankali kan damammakin bayan COVID-19 da kulla dangantakar Najeriya da Faransa musamman a bangaren tsaro da tattalin arziki ke da shi.

Ya nuna bukatar shugabannin kasashen Sahel su gabatar da hadin kai don yin kira ga sauran kasashen yamma, musamman Burtaniya da Amurka da Tarayyar Turai, don ƙarin taimakon soja da na jin kai.

A wani labarin kuma, Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Mallam Abubakar Nuhu Fikpo matsayin Dirakta Janar na ma'aikatar samar da aikin yi watau NDE.

Hakazalika Buhari ya nada Kwamred Issa Aremu a matsayin Dirakta Janar da Kwalejin Kwadago na kasa (NILS).

Sakon shugaban kasan na kunshe cikin jawabin da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya saki da yammacin Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel