Da Dumi-Dumi: Buhari Zai Sake Cin Bashin N2.342tr Wa Najeriya Daga Kasar Waje

Da Dumi-Dumi: Buhari Zai Sake Cin Bashin N2.342tr Wa Najeriya Daga Kasar Waje

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kudurta sake cin bashin N2.342trn don gudanar da wasu ayyuka a Najeriya.

Shugaban majalisar dattawa a Najeriya, Ahmed Lawan ne ya karanta takardar da shugaba Muhammadu Buhari ya aike wa majalisar a zamansu na yau Talata 18 ga watan mayu.

Legit.ng Hausa ta gano majalisar dattawan Najeriya ta wallafa bukatar shugaban kasan a shafin Twitter cewa shugaba Buhari na mika , "Kudurin Majalisar Kasa don aiwatar da karbar bashin waje na dala biliyan 2.18 a cikin Dokar Kasafin Kudin 2021"

Da Dumi-Dumi: Buhari Za Saki Cin Bashin N2.342tr Wa Naheriya Daga Kasar Waje
Da Dumi-Dumi: Buhari Za Saki Cin Bashin N2.342tr Wa Naheriya Daga Kasar Waje Hoto: africa.cgtn.com
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel