‘Yan Twitter sun jero sunayen wadanda Jonathan ya yi wa azaba kafin ya bar mulki a 2015

‘Yan Twitter sun jero sunayen wadanda Jonathan ya yi wa azaba kafin ya bar mulki a 2015

- Dr. Goodluck Jonathan ya yi ikirarin bai gallazawa kowa da yake mulki ba

- An maida martani, an jero wasu laifuffuka da ake zargin gwamnatinsa da su

- A mulkin Jonathan ne aka tsige Sanusi Lamido daga kujerar gwamnan CBN

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan, ya jawo abin magana bayan ya ce bai taba amfani da kujerar mulki, ya zalunci kowa ba.

Jaridar The Cable ta rahoto yadda mutane su ke ta maida wa Goodluck Jonathan martani a shafin Twitter, a kan abubuwan da ya yi da yake kan mulki.

Goodluck Jonathan ya yi wannan jawabi ne a wajen bikin cikan babban limamin cocin Rock of Ages Christian Assembly, Charles Osazuwa shekara 50.

KU KARANTA: An fara yi wa Jonathan kamfe ya nemi takara a 2023

Wani Bawan Allah mai suna Modibbo Sanusi ya tado batun tsige Sanusi Lamido Sanusi da gwamnatin Jonathan ta yi a babban bankin CBN a 2014.

Wani mutum ya jero irin munanan damkar da aka rika yi wa ‘yan jarida a lokacin da Goodluck Jonathan yake mulkin Najeriya tsakanin 2010 da 2015.

“Ji karya karara da safiyar Litinin! Mutanen da kai Jonathan ka azabtar a lokacin da ka ke mataimakin gwamna, gwamna, mataimakin shugaban kasa da shugaban kasa, sun isa su cike katon kamus.” Inji wani.

Wani mai amfani da Twitter ya rubuta: “Ina batun Sanusi Lamido? Ina maganar tsare gwamna Rotimi Amaechi a cikin gidan gwamna?”

KU KARANTA: Jonathan ya yi wa El-Rufai kaca-kaca kan zargin musguna masa

‘Yan Twitter sun jero sunayen wadanda Jonathan ya yi wa azaba kafin ya bar mulki a 2015
Dr. Goodluck Jonathan Hoto: thisdaylive.com

Wani ya ce: “Shekarar 2015 fa kamar jiya, kun dauka mun manta ne. Ku fada wa yaran da su ka yi wayau bayan 2015 wannan shirmen."

Shi kuma wani mutumi cewa ya yi ana wasa da tarihi a kasar nan, nan gaba har ‘ya ‘yan Marigayi Janar Sani Abacha za su fito suna da bakin magana.

Wannan kuwa ya yi dariya: “Buhahaha... “Ya ce: “Yadda lokaci ke sa a manta da komai!”

A jiya an ji cewa Gwamna Ifeanyi Okowa ya ce nan da wata daya rak za a buga gangar siyasar 2023 a jihar Delta, har ya fara maganar wanda zai zama magajinsa.

Ifeanyi Okowa ya ce a cikin watan Yuni zai fadi wanda zai zama sabon Gwamnan jihar Delta. Amma gwamnan mai-ci ya bada wasu sharudan da magajinsa zai cika.

Asali: Legit.ng

Online view pixel