Goodluck Jonathan ya yi wa El-Rufai kaca-kaca, ya fadi abin da ya jawo rikicinsu a 2011

Goodluck Jonathan ya yi wa El-Rufai kaca-kaca, ya fadi abin da ya jawo rikicinsu a 2011

- Goodluck Jonathan ya ce zargin musgunawa Nasir El-Rufai ba gaskiya ba ne

- Tsohon Shugaban ya ce da farko Gwamna El-Rufai ya nuna ya na tare da shi

- Jonathan ya fadi dalilin da ya sa Jami’an tsaro suka yi ram da Nasir El-Rufai

Tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan, ya karyata zargin da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya jefe sa da shi na nuna masa tsangwama.

A jiya Goodluck Jonathan ya fitar da jawabi ta bakin wani tsohon hadiminsa, Reno Omokri, ya ce zargin tsohon Ministan ba komai ba ne face kanzon kurege.

Goodluck Jonathan yake cewa babu gaskiya a zargin da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ke yi masa na cewa gwamnatinsa ta nemi ta cafke shi.

KU KARANTA: El-Rufai: Na fuskanci tsangwama daga Ƴar’Adua da Jonathan

Ya ce: “Idan ‘Yan Najeriya za su tuna, Malam Nasir El-Rufai ya dawo daga korar da ya yi wa kansa da kansa ne a lokacin mulkin shugaba Umar Musa Yar’Adua.”

“El-Rufai ya dawo Najeriya ne a ranar 5 ga watan Mayu, 2010, ranar da ‘Yaradua ya rasu. Ya dawo ne da sa ran shugaba Jonathan zai ba shi damar ya sarara.”

“Kwanaki shida rak da dawowarsa, El-Rufai ya zauna da Jonathan a Aso Rock, ya zanta da ‘yan jarida, ya yi maganar da ba a tambayesa ba.” Inji Reno Omokri.

Omokri ya ce a nan El-Rufai ya yi kira ga Jonathan ya yi takara a 2011, ya ce zai goya masa baya.

KU KARANTA: Wasu 'yan bindiga sun Ƙona ofishin 'Yan sanda a Abia

Goodluck Jonathan ya yi wa El-Rufai kaca-kaca, ya fadi abin da ya jawo rikicinsu a 2011
Goodluck Jonathan da Nasir El-Rufai Hoto: punchng.com
Asali: UGC

“Bayan nan, shugaban kasa ya bayyana Namadi Sambo a matsayin mataimakinsa a ranar 13, ga watan Mayu, daga nan El-Rufai ya fara jin haushi."

Ya cigaba da cewa: "...(El-Rufai) ya shirya barin PDP, ya na cin mutuncin gwamnatin Jonathan.”

Jawabin ya ce: “Duk da surutan El-Rufai, Jonathan bai biye masa, ya nemi ya yi fadi da shi ba.”

“Sai jami’an tsaro suka samu rahoto da ke nuna El-Rufai ya na neman tunzura al’umma da nufin ya jawo a daure shi, saboda hakan ya kara masa farin jini.”

A sakamakon sharrin da El-Rufai ya rika yi, ya na zargin gwamnatin Jonathan da hannu a rikicin Boko Haram, Omokri ya ce hakan ya sa aka yi ram da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng