Saura shekara 2 ayi zaben 2023, Gwamnan PDP ya ce zai bayyana wanda zai zama Magajinsa

Saura shekara 2 ayi zaben 2023, Gwamnan PDP ya ce zai bayyana wanda zai zama Magajinsa

- Gwamna Ifeanyi Okowa ya fara maganar zaben 2023 tun a yanzu

- Ifeanyi Okowa ya ce a watan Yuni ne zai fadi wanda zai gaje shi

- Gwamnan ya fadi abin da yake so a kan wanda zai zama Gwamna

Jaridar Punch ta rahoto Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, yace a watan gobe, zai fara shirye-shiryen zakulo da wanda zai gaje shi a 2023.

Mai girma Ifeanyi Okowa yake cewa za ayi adalci da gaskiya wajen fito da gwamnan gobe a Delta.

Gwamna Ifeanyi Okowa ya tabbatar da cewa duk wanda zai zama gwamna bayansa, sai ya yi kokari wajen ganin kowa a matsayin na sa a Delta.

KU KARANTA: PDP ta soma fafe gorar 2023 domin ta hambarar da gwamnatin APC

Ifeanyi Okowa wanda yake cikin shekara ta biyu a wa’adinsa na karshe zai bar ofis ne a Mayun 2023.

“Ina kira ga mutanenmu cewa wannan lokaci ne da za a hada-kai, ayi tunani iri daya, kuma ina so in sake tabbatar maku nan da wata daya za a fara siyasa.”

“Kuma ga wadanda suke tsilla-tsilla saboda ‘na-goro’ da ake ba su, muna jan-kunnensu.”

“Na gode wa Allah da ‘danuwa na, Elumelu ya gayyaci kansiloli 80 daga kananan hukumomi hudu a mazabarsa, muna farin ciki da wannan.” inji Sanata Okowa.

KU KARANTA: Ya kamata a ce an yi waje da Buhari tuni - Adebanjo

Saura shekara 2 ayi zaben 2023, Gwamnan PDP ya ce zai bayyana wanda zai zama Magajinsa
Gwamna Ifeanyi Okowa
Asali: Twitter

Okowa yake cewa wasu na ganin bai dace mutanen Delta ta Arewa, musamman ‘Yan Aniocha/Oshimili su samu kansiloli 20 a kowace karamar hukuma ba.

Gwamnan ya ce masu wannan ra’ayi ne suke mika wa ‘yan siyasa kudi domin sayen ra’ayinsu. “Masu kitsa wannan aiki, su ne ke ba mutanenmu kudi.”

“Duk wanda zai zo ya yi mulkin jihar nan, ya shirya yin adalci da gaskiya a kan kowane lamari.”

“Muna son wanda zai zo Asaba, ya dauka cewa babbar birnin ce, a maimakon wanda zai rika ganin ajiye babban birni a Asaba ba daidai bane.” Inji Gwamnan.

Wani jigon Jam’iyyar APC a Kudancin Najeriya, Hon. Saheed Akinade-Fijabi ya ce zaben 2023 babu tabbas, sai dai lokacin ya yi kurum za a gane yadda za ta kaya.

Saheed Akinade-Fijabi ya na ganin babu tabbacin Jam’iyyar APC za ta iya kai labari ba tare da an ba Bola Tinubu tuta ba, ya ce hakan zai iya jawo masu cika a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel