Hoton mutum 2 suna yi wa Sanusi II sujada ya janyo cece-kuce, tsohon basaraken ya magantu

Hoton mutum 2 suna yi wa Sanusi II sujada ya janyo cece-kuce, tsohon basaraken ya magantu

- Tsohon sarkin Kano, Mai Martaba Muhammadu Sanusi II yayi bayani a kan hoton da aka ga wasu na yi masa sujada

- Kamar yadda ya bayyana, ya kammala limanci la'asar ne yake tashi, su kuma suna rama raka'a da basu samu ba

- Basaraken yace idan za a lura akwai dardumar sallah a bayansa yayin da ya tashi hawa kujera don fara karatun Madaarij-us-Saalikeen

Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II yayi bayani a kan hotunansa da suka janyo cece-kuce inda wasu mutum biyu ke masa sujada.

Tsohon basaraken, wanda cikin kwanakin nan aka nada shi Khalifan Tijjaniya a Najeriya, ya sha caccaka a kafafen sada zumuntar zamani a kan hoton.

Yayin da wasu ke kushe yadda mutum biyun ke masa sujada, wasu sun dauka laifin kacokan sun dora a kan sarkin da ya bar su.

KU KARANTA: 'Yan Najeriya ne ke ta rokona in fito takarar shugabancin kasa, Yahaya Bello

Hoton mutum 2 suna yi wa Sanusi II sujada ya janyo cece-kuce, tsohon basaraken ya magantu
Hoton mutum 2 suna yi wa Sanusi II sujada ya janyo cece-kuce, tsohon basaraken ya magantu. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Amma a wata tattaunawar waya da Daily Nigerian tayi da sarkin, ya ce wannan sujada da mutane biyun ke yi ba gaisuwa bace garesa, sallah suke yi.

Yace an dauka hoton ne a yayin da suke dab da fara karatun Madaarij-us-Saalikeen wanda suke farawa da karfe 4:15 na yamma bayan sallar la'asar.

"Na saba fitowa wurin karfe 4 na yamma domin limancin sallar la'asar, bayan nan sai mu fara karatun Madaarij-us-Saalikeen zuwa karfe 4:15 na yamma.

"Wadannan mutane biyu da kuke gani sun zo ne yayin da muke sallah sai suka rasa raka'a. Yayin da na tashi in koma kujerata bayan limanci, wani ya dauka hoton su kuma suna sujada.

"Idan zaku duba da kyau, zaku hango dardumata. Babu dalilin da zai sa in bar wani yayin min sujada," basaraken yayi bayani.

KU KARANTA: Na Allah basu karewa: Dan sanda ya mayar da N1.2m da ya tsinta wurin hatsari a Kano

A wani labari na daban, akwai zargin cewa ran jarumi Lawan Ahmad yayin da ya zabgawa jaruma Hannatu Usman mari yayin da ake wurin daukar fim mai dogon zango mai suna 'Bugun Zuciyar Masoya'.

Lamarin ya faru ne a Kano yayin da ake shirye-shiryen daukar shirin kashi na 37 wanda jarumar ke fitowa da suna Nafisa.

Wata majiya mai karfi ta sanar da mujallar fim cewa ran Hannatu ya kai matuka a baci bayan an sanar da ita cewa labarin baya bukatarta kuma za a sauyata da wata jaruma saboda hadari da tayi a fim din.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng