Ka nemi kujerar Buhari a 2023, za mu baka goyon baya – Mata sun fadawa Gwamnan Arewa

Ka nemi kujerar Buhari a 2023, za mu baka goyon baya – Mata sun fadawa Gwamnan Arewa

- Wasu mata sun taso Gwamna jihar Kogi a gaba ya nemi kujerar Shugaban kasa

- Matan suna ganin Yahaya Bello ne wanda ya dace ya gaji Muhammadu Buhari

- Kungiyar tace a Gwamnatin Yahaya Bello ne mata suka fara samun SSG da ADC

Wasu mata daga yankin kudu maso yammacin Najeriya sun yi kira ga gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya fito takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a karshen makon nan cewa wadannan mata sun tabbatar wa gwamnan cewa za su mara masa baya a zabe mai zuwa.

Kamar yadda yake ikirarin sauran mutane suna tare da shi, matan yankin Yarbawan sun ce suna tare da gwamnan da zai kammala wa’adinsa a karshen 2023.

KU KARANTA: Bana neman takarar Shugaban kasa a 2023 - Osinbajo

Matan sun yi wannan kira a taron farko da kungiyar South-West Women Arise for Nigeria ta shirya domin wayar da kan al’uumma a kan hadin-kai a Legas.

An yi wannan taro ne a wani otel da ke garin Legas a ranar Juma’a 14 ga watan Mayu, 2021.

Wasu matan yankin na Kudu maso yamma sun yi taron ne a karkashin jagorancin Bolanle Idowu, inda ta yaba wa kokarin da gwamna Yahaya Bello yake yi.

‘Yan kungiyar South-West Women Arise for Nigeria suka ce, suna tare da Yahaya Bello saboda yadda ya rika ba mata mukamai masu tsoka a gwamnatinsa.

KU KARANTA: Bello ya bayyana wanda Bola Tinubu zai marawa baya a 2023

Ka nemi kujerar Buhari a 2023, za mu baka goyon baya – Mata sun fadawa Gwamnan Arewa
Gwamna Yahaya Bello
Asali: Facebook

Misis Bolanle Idowu ta yi jawabi a madadin sauran matan, ta nuna cewa ba su goyon bayan kiran da ake yi na raba Najeriya, ta ce hakan ba mafitar kirki ba ce.

“Ba lokacin raba gari ba ne. A matsayinmu na mata, muna da ikon kawo hadin-kai.” Inji Idowu.

Matan suka ce Yahaya Bello ne gwamnan farko da ya zabi mace a matsayin dogarinsa a tarihin Najeriya, sannan ya ba mace kujerar sakatariyar gwamnatin jiha.

Bugu da kari, duka mataimakan shugabannin kananan hukumomi da ke jihar Kogi mata ne.

Za a gudanar da babban zaben shugaban kasa a Najeriya ne a farkon 2023, watanni kusan goma kafin Yahaya Bello ya sauka daga kan kujerar gwamnan Kogi.

Gwamna Ifeanyi Okowa ya ce nan da wata daya rak za a buga gangar siyasar 2023 a jihar Delta, har ya fara maganar wanda zai zama magajinsa a gidan gwamnati.

Ifeanyi Okowa ya ce a cikin watan Yuni zai fadi wanda zai zama sabon Gwamnan Delta. Amma gwamnan mai-ci ya bada wasu sharudan da magajinsa zai cika.

Asali: Legit.ng

Online view pixel