Gwamna Yahaya Bello ya bayyana wanda Bola Tinubu zai marawa baya a zaben 2023
- Yahaya Bello ya bayyana cewa matashi zai samu goyon-bayan Bola Tinubu
- Gwamnan jihar Kogi ya na ganin Bola Tinubu ba zai shiga takarar 2023 ba
- Bello ya ce ana girmama Tinubu, amma duk da haka ba zai nemi mulki ba
Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya ce ya yi imani jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ba zai nemi takarar shugaban kasa a 2023 ba.
Gwamna Yahaya Bello ya bayyana cewa tsohon gwamnan na jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu zai goyi-bayan matashin ‘dan takara ne a zaben mai zuwa.
Har yanzu Bola Tinubu bai sanar da Duniya ya na harin kujerar shugaban kasa ba, amma gwamnan na Kogi ya nuna sha’awar mulkin kasar nan.
KU KARANTA: PDP ta yi karin-haske game da maganar dakatar da Babangida Aliyu
Da aka yi hira da Yahaya Bello a BBC Pidgin, an tambaye shi game da wanda ya ke ganin zai fi dace wa da shugaban kasa tsakanin shi da jagoran na APC.
Yahaya Bello ya ce Bola Tinubu shugaba ne wanda yake kafa mutae a kan mulki, don haka ya ce kusan na APC zai gwammace ya goyi-bayan matashi a 2023.
“Jagoran jam’iyyarmu, Tinubu, dattijo ne da kowa ya ke ganin darajarsa, har ni. Na san cewa jagora ne mai basira, ya kawo shugabanni da yawa a kasar nan.”
“Shi mai daura mutane a kan kujerar mulki ne. Kuma na san cewa ya na so kasar nan ta kama hanyar alkibla. Ya san abubuwan da zai iya, ya san iyakarsa.”
KU KARANTA: Bola Tinubu ya ce Buhari ya fito da kudi, ya daina mako
“Ya san wanda zai iya rike kasar nan har ya kammala wa’adinsa. Na yarda da aikinsa.” inji Bello.
Bello ya sake jaddada cewa matasa da mata da sauran ‘yan Najeriya su na kiran shi ya fito takara, ya ce bai taba kashe ko sisi wajen buga allunan neman takara ba.
A jiya ne aka ji Aminu Abdussalam Gwarzo ya na sukar taron Bola Tinubu da aka yi a Kano. Jagoran adawar ya caccaki bikin, ya ce akwai wani lauje a cikin nadi.
Kwamred Aminu Gwarzo ya ce siyasa ce kurum ta sa aka zabi ayi bikin taya Asiwaju Bola Tinubu murnar cika shekara 69 da haihuwa a jihar su ta Kano, ba komai ba.
Asali: Legit.ng