Da Ɗumi-Ɗumi: Sarki Mai Daraja Ta Ɗaya Ya Mutu a Adamawa

Da Ɗumi-Ɗumi: Sarki Mai Daraja Ta Ɗaya Ya Mutu a Adamawa

- Sarkin Mbula, Mai Martba Joel J. Fwa ya riga mu gidan gaskiya

- Marigayin ya rasu ya bar matar aure daya da yara guda 10

- Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya yi ta'aziyya ga masarautar Mbula

Masarautar Mbula da ke jihar Adamawa ta sanar da rasuwar Mai Martaba Joel J. Fwa, Murum Mbula kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Marigayin ya rasu yana da shekaru 81 ya kuma bar matan aure daya da yara 10.

Gwamnan jiharAdamawa Ahmadu Fintiri ya mika sakon ta'ziyyarsa ga masarautar Mbula, Iyalan Sarki da daukakin al'ummar masarautar Mbula game da rasuwar sarkin.

Da Ɗumi-Ɗumi: Sarki Mai Daraja Ta Ɗaya Ya Mutu a Adamawa
Da Ɗumi-Ɗumi: Sarki Mai Daraja Ta Ɗaya Ya Mutu a Adamawa. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Falaɗinawa Sun Harbo Mana Roka 3,150 Daga Gaza, Isra'ila

"Na yi matukar bakin cikin samun labarin rasuwar Mai Martaba Murum Mbula J.J. Fwa a ranar Lahadi," in ji shi.

Ya bayyana marigayin sarkin na Mbula a matsayin rumbun Ilimi wanda ya sadaukar da rayuwarsa wurin yi wa al'umma hidima da bautan Allah.

Gwamnan ya ce rasuwar Murum babban rashi ne ga kasar baki daya musamman yanzu da kallubalen tsaro ke adabar mutane.

Ya yi kira ga al'ummar masarautar Mbula da iyalan sarkin da dukkan mutanen damawa su dangana ga Allah su jure wannan babban rashin.

"Mun rasa babban jigo da ake darajawa kuma da ga Adamawa kuma basarake da ya sadaukar da rayuwarsa wurin yin ayyukan da ba za a manta da su ba."

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Ƴan Bindiga Sun Sace Farfesa Da Mijinta a Gidansu

Fintiri ya yaba da ayyukan da marigayin ya yi a gwamnati da kuma masarautun gargajiya yana mai cewa ya bada muhimmiyar gudun mawa wurin tabbatar da zaman lafiya da cigaban mutanen Numan da jihar Adamawa baki daya.

Gwamnan ya yi addu'a Allah ya jikan sarkin ya gafarta masa, ya kara da cewa, "sai an samu jarumi kafin zai iya maye gurbinsa."

A wani labarin daban, jami'an yan sanda sun halaka a kalla yan ta'addan Boko Haram takwas da suka yi yunkurin kai wa mazauna garin Maidguri, babban birnin jihar Borno hari a yammacin ranar Talata, PRNigeria ta ruwaito.

Legit.ng ta ruwaito cewa yan ta'addan sun shiga cikin garin da motocci masu bindiga da babura da dama a ranar Talata yayin da musulmi ke shirin yin bude bakin azumin Ramadan. 'Yan Sanda Sun Kashe 'Yan Boko Haram 8 Da Suka Kai Hari Maiduguri.

Wata majiyar sirri ta shaida wa PRNigeria cewa yan ta'addan suna cikin kona gidajen mutane ne a Jiddari Polo a yayin da yan sandan karkashin jagorancin CSP Mohammed Ibrahim suka iso unguwar da mota mai bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel