Matsananciyar Yunwa Na Kashe Ƴan Nigeria, PDP Ta Faɗawa Buhari
- Jam'iyyar hamayya ta PDP ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya magance yunwa a kasar
- Kola Ologbondiyan, mai magana da yawun jam'iyyar na ƙasa ya ce yunwa na halaka ƴan kasar bayan galabaitar da su
- Jam'iyyar na PDP ta bawa Buhari shawarwarin hanyoyin da zai bi domin warware matsalar ta yunwa a kasar
Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a jiya Lahadi ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya ɗauki matakan magance ƙarancin abinci a ƙasar, Daily Trust ta ruwaito.
Jam'iyyar ta PDP a sanarwar da ta fitar ta bakin kakakinta Kola Ologbondiyan ta ce ƙarancin abinci yana kashe ƴan Nigeria.
DUBA WANNAN: ICPC Ta Fara Farautar Sirikin Buhari Ruwa a Jallo
Ta ce fiye da ƴan Nigeria miliyan 82.9 ba su iya samun abinci a kullum saboda gwamnati mai ci yanzu ta gaza ɗaukan matakan haɓɓaka bangaren samar da abinci, hakan ya janyo ƙarancin abinci da tashin farashinsu ta yadda ƴan Nigeria ba za su iya siya ba.
Ta bukaci Buhari ya ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalar yunwa ta hanyar buɗe rumbun ajiyar abinci don saukar da farashinsu.
Ta kuma ce gwamnatin tarayya ta samar da tsaro domin manoma su iya komawa gonakin su ba tare da tsoron rashin tsaro ba.
Har wa yau, jam'iyyar hammayar ta bukaci Buhari ya bada tallafi ga ƙananan sana'o'i domin su biya albashi su haɓɓaka ayyuka.
KU KARANTA: Sarkin Muri Ya Umurci Mutanen Masarautarsa Su Yi Fito-Na-Fito Da Ƴan Bindiga
Ta koka cewa a yanzu, "Nigeria ce ƙasa ta 98 cikin 107 a jerin kasashen da yunwa ya fi adabar mutane, ga kuma rashin abinci, rashin kuɗi a hannun mutane, rashin ayyukan yi kashi 33.3 cikin 100 da haihuwar farashin kayan abinci 22.95 da ya haifar da mace-mace.
"A yau a gwamnatin APC, buhun shinkafa da ake sayarwa N8,000 a gwamnatin PDP ya koma N30,000, mudun gari ya tashi daga N150 ya koma N500, wake daga N250 zuwa N800; mudin masara da dawo sun tashi daga kimanin N150 zuwa 400, kilon nama daga N800 zuwa N2,300," in ji PDP
A wani labarin daban kun ji cewa gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin ta tabbatar da cewa mutane shida sun mutu sakamakon wata bakuwar cuta a karamar hukumar Minjibir a jihar, Vangaurd ta ruwaito.
Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Ibrahim-Tsanyawa wanda ya tabbatar da hakan ya ce wasu mutum 46 da suka kamu da cutar na jinya a asibiti.
Ibrahim-Tsanyawa ya ce cutar ta bulla ne a kauyen Gandun Koya da ranar 7 ga watan Mayu kuma ta yadu zuwa garuruwan da ke makwabtaka da ita.
Asali: Legit.ng