Ganduje ya saka hannu a kan sabuwar dokar masarautu ta Kano

Ganduje ya saka hannu a kan sabuwar dokar masarautu ta Kano

- Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, yasa hannu a kan dokar da ta mayar da Sarkin Kano shugaban majalisar sarakuna

- Yanzu haka Sarki Aminu Bayero ya zama shugaban majalisar sarakunan masarautar Kano na dindindin

- Gwamnan jihar Kano, ya sa Gidan Shettima ya zama ofishin Sarkin, saboda wurin bashi da nisa da fadarsa

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya sa hannu akan dokar jihar, wadda ta mayar da Sarkin Kano ya zama shugaba na dindindin ga majalisar sarakunan jihar.

Kafin a gyara dokar ta amince da karba-karbar shugabancin a tsakanin 'yan majalisar 5 na jihar a lokacin da tubabben Sarki Muhammadu Sanusi II yana sarautar Kano.

Sakataren yada labarai na gwamnan, Abba Anwar, a wata takarda yace, "Bayan sa hannu a wannan dokar, Aminu Ado Bayero ya zama shugaban majalisar sarakuna, sannan Gidan Shettima ya zama ofishin majalisar, wanda ba shi da nisa daga fadar sarkin."

"Kafin a gyara wannan dokar, masarautar nada masu nadin sarki 4, daga masarautu 5. Yanzu kuwa, muna da 'yan majalisar sarakuna 5. Mun yi hakan ne don juya duk wani mummunan lamari da zai faru idan za'a sake zabar wani sarki," kamar yadda takardar ta zo.

Ya ce kwanan nan za a rantsar da Sarkin a matsayin shugaban majalisar Sarakuna a ofishinsa, wanda yanzu haka ake gyarawa.

KU KARANTA: EndSARS: Babu bukatar cigaba da zanga-zanga don kun samu abinda kuke so

Ganduje ya saka hannu a kan sabuwar dokar masarautu ta Kano
Ganduje ya saka hannu a kan sabuwar dokar masarautu ta Kano. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan daba dauke da makami sun kai wa masu zanga-zanga hari a Abuja

A wani labari na daban, Babajide Sanwo-Olu, gwamnan jihar Legas ya ce gwamnatin jihar ta ware kudi har naira miliyan 200 domin biyan diyya ga iyalan da jami'an rundunar SARS suka kashe musu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin jawabi ga masu zanga-zangar a gaban majalisar jihar Legas a ranar Talata. Sanwo-Olu ya ce an ware kudaden ne domin tallafa wa iyalan wadanda 'yan sandan suka kashe bisa kuskure.

Ya ce an samo jerin sunayen wadanda 'yan sandan suka kashe kuma ana sake bincikawa domin tabbatar da cewa ba a cire sunan kowa ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel