Gwamnati ta amince da bude gidajen shan Shisha a kasar Saudiyya

Gwamnati ta amince da bude gidajen shan Shisha a kasar Saudiyya

- An fara sassauta dokokin kulle a kasar Saudiya yayinda Korona ta fara sauki

- Hakazalika Saudiyya ta sanar da cewa za'a gudanar da hakkin Hajji bana

An amince a sha shisha a wuraren shan gahawa a Saudiyya daga ranar Litinin yayin da ake sassauta dokar kullen korona a ƙasar, rahoton Saudi Gazzete.

Bayan shekara guda, Saudiyya ta fara sassauta dokokin kulle sakamakon annobar cutar Korona.

Cikin sharrudan da ma’aikatar kula da birane da karkara ta gindaya domin amincewa mutum ya shiga shagon Shisha shine ya kasance ya yi rigakafin Korona.

Hakazalika wajibi ne dukkan ma'aikatan shagunan su rika yin gwajin korona mako-mako.

Hakazalika, wajibi ne bada tazara kuma a sarari za'a sayar.

Bayan haka, sau daya za'a yi amfani da tiyo guda wajen shan Shisha kuma kada mutum sama da biyar su sha a lokaci guda.

Ma'aikatar ta bayyana sharruda ne a manhajarta na Tawakkalna

DUBA NAN: Muna namijin kokarin wajen magance matsalar tsaro, ina fatan yan Najeriya zasu gane, Buhari

Gwamnati ta amince da bude gidajen shan Shisha a kasar Saudiyya
Gwamnati ta amince da bude gidajen shan Shisha a kasar Saudiyya Hoto: Saudi Gazzete
Asali: Facebook

DUBA NAN: Rikici da Falasdinawa: Kamfanonin jirage sama 7 sun dakatad da zuwa Isra'ila

A bangare guda, Yariman Saudiyya mai jiran gado Muhammad bin Salman bin Abdulaziz da mataimakin Firaminista da kuma ministan tsaro sun tattauna da shugaban sojin Chadi Mahamat Idriss Deby ta wayar tarho a ranar Lahadi.

Alarabiya News ta ruwaito cewa, Yarima bin Salman ya yi wa Janar Mahamat Deby ta’aziyyar rasuwar mahaifinsa Idriss Deby wanda ya rasu a ranar Litinin sakamakon samun wasu raunuka a fagen daga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng