Haramta kiwo: Ndume yayi martani mai zafi ga Gwamnoni 17 na kudanci

Haramta kiwo: Ndume yayi martani mai zafi ga Gwamnoni 17 na kudanci

- Sanata mai wakiltar mazabar Borno ta kudu, Ali Ndume, ya caccaki hukuncin gwamnoni 17 na kudancin kasar nan

- A ranar Talata ne suka yi taro inda suka haramta kiwo dabbobi a bude tare da safararsu a kasa saboda kalubalen tsaro

- Ndume ya ce hana kiwo ba shine hanyar shawo kan matsalarsu ba domin matsalar tsaron kassar nan tana daji ne

Ali Ndume, sanata mai wakiltar mazabar Borno ta kudu a majalisar dattawa, ya soki hukuncin gwamnonin kudu na haramta kiwo a bude tare da hana yawon shanu a kasa.

Gwamnonin sun yanke wannan hukuncin ne a wani taro da suka yi a jihar Delta a ranar Talata.

Kamar yadda suka ce, haramta kiwon zai hana fadace-fadacen da ake yawan samu tsakanin manoma da makiyaya kuma hakan zai inganta tsaron yankin, The Cable ta ruwaito.

Amma a yayin jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Laraba, Ndume yace gwamnonin sun fara neman dorawa wasu laifi a yayin shawo kan matsalarsu.

KU KARANTA: Dan sandan da 'yan bindigan daji suka harba ya sheka lahira a asibiti

Haramta kiwo: Ndume yayi martani mai zafi ga Gwamnoni 17 na kudanci
Haramta kiwo: Ndume yayi martani mai zafi ga Gwamnoni 17 na kudanci. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Labari da duminsa: Ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a Saudiyya

"Wannan neman dorawa wasu laifin ba zai shawo kan matsalar ba," shugaban kwamitin kula da rundunar soji na majalisar dattawa yace.

"Gwamnoni ne shugabanni a fannin tsaron jiharsu, toh me yasa ake magana kan shugaban kasa ba tare da fara magana a kansu ba? Gwamnoni sun fara waskewa daga al'amarin, matsalar ba kiwo dabbobi a bude bane.

"Matsalar ita ce tsaro. Da yawa daga cikin matsalolin tsaron dake addabar Najeriya suna daji ne.

"Muna da nau'ikan matsalolin tsaro hudu. Akwai 'yan ta'adda dake arewa maso gabas, IPOB, ESN dake samar da rashin tsaro a yankin kudu maso gabas, akwai kuma 'yan bindiga da suka addabi arewa maso yamma.

“A yankin arewa ta tsakiya ne kadai akwai fadan manoma da makiyaya. Matsaloli kadan ne akwai a yankin kudu maso yamma, sai dai rikicin manoman da makiyaya da kuma masu rajin samun kasar Yarabawa."

A wani labari na daban, 'yan sanda a jihar Binuwai sun bankado wasu kaburburan sirri a karamar hukumar Katsina-Ala ta jihar.

Daily Trust ta ruwaito cewa an samo ire-ire kaburburan nan a garin ZakiBiam dake karamar hukumar Ukum tun a watan Oktoban 2019, makonni uku bayan an gano wasu da ake zargin 'yan kungiyar asiri ne ke kashe mutane tare birnesu a ciki a karamar hukumar Ushongo ta jihar.

Wannan gano kaburburan da aka yi ya biyo bayan kama wasu miyagun gagararrun 'yan ta'adda biyu da aka yi wadanda ake zargin yaran Azonto ne, mataimakin marigayi Terwase Akwaza a yankin Katsina-Ala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel