Ganduje Ya Yi Wa Fursunoni 123 Afuwa Albarkacin Ƙaramar Sallah

Ganduje Ya Yi Wa Fursunoni 123 Afuwa Albarkacin Ƙaramar Sallah

- Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano ya saki fursunoni 123 daga gidajen gyaran hali

- Gwamnan ya ce ya yi musu wannan afuwan ne saboda albarkacin bikin karamar Sallah

- Gwamnan ya shawarci wadanda aka saki su sauye halayensu su kuma rika yi wa kasa addu'a

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya saki fursunoni 123 daga gidajen gyaran hali a fadin jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ganduje, wanda ya aka saki fursunonin a gabansa daga gidan gyaran hali na Goron Dutse a ranar Alhamis ya ce anyi musu wannan karamcin ne albarkacin bikin karamar Sallah.

Ganduje Ya Yi Wa Fursunoni 123 Afuwa Albarkacin Ƙaramar Sallah
Ganduje Ya Yi Wa Fursunoni 123 Afuwa Albarkacin Ƙaramar Sallah. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sarkin Muri Ya Umurci Mutanen Masarautarsa Su Yi Fito-Na-Fito Da Ƴan Bindiga

Ya ce an zabi wadanda suka amfana da afuwar ne bisa la'akari da yanayin laifukansu da kuma alamun da ke nuna cewa sun gyaru sun sauya halayensu.

Gwamnan ya ce ya yanke shawarar kai ziyara gidan yarin ne domin nuna wa fursunonin cewa gwamnatin jihar ta san da zamansu kuma suma ana daukansu matsayin yan jiha.

Ganduje ya ce an saki fursunonin ne bisa tsarin gwamnatin tarayya na kokarin ganin an rage cinkoso a gidajen gyaran hali a kasar.

Ya shawarci wadanda aka saki daga gidan gyaran halin su sauya tsarin rayuwarsa sannan su yi wa kasa addu'an zaman lafiya da cigaba.

Gwamnan ya kuma bawa kowannensu N5,000 a matsayin kudin mota zuwa gidajensu.

KU KARANTA: Hoton Hadiza Bala Usman Da El-Rufai a Fadar Sarkin Zazzau Ya Janyo Maganganu

Tunda farko, Kwantrola Janar na Gidajen Gyaran Hali na Kano, Suleiman Suleiman ya yi wa gwamnan godiya saboda sakin fursunoni da dama tun hawansa mulki.

Suleiman ya shawarci fursunonin da aka saki su gaji aikata wani laifin da zai saka a dawo da su gidan.

Ganduje ya kuma ziyarci gidajen kananan yara a birnin Kano duk cikin bikin na Sallah.

A wani labarin daban, jami'an yan sanda sun halaka a kalla yan ta'addan Boko Haram takwas da suka yi yunkurin kai wa mazauna garin Maidguri, babban birnin jihar Borno hari a yammacin ranar Talata, PRNigeria ta ruwaito.

Legit.ng ta ruwaito cewa yan ta'addan sun shiga cikin garin da motocci masu bindiga da babura da dama a ranar Talata yayin da musulmi ke shirin yin bude bakin azumin Ramadan. 'Yan Sanda Sun Kashe 'Yan Boko Haram 8 Da Suka Kai Hari Maiduguri.

Wata majiyar sirri ta shaida wa PRNigeria cewa yan ta'addan suna cikin kona gidajen mutane ne a Jiddari Polo a yayin da yan sandan karkashin jagorancin CSP Mohammed Ibrahim suka iso unguwar da mota mai bindiga.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel