Rashin tsaro: Gwamnonin Kudu sun haramta kiwo a bude, sun bukaci Buhari yayi wa kasa jawabi

Rashin tsaro: Gwamnonin Kudu sun haramta kiwo a bude, sun bukaci Buhari yayi wa kasa jawabi

- Gwamnonin yankin kudancin kasar nan guda 17 sun yi taro a kan halin da kasar nan ke ciki a Delta

- A karshen taron, sun haramta kiwo a kan tituna kuma sun yi kira ga Buhari da yayi jawabi ga 'yan Najeriya

- Gwamnonin sun tabbatar da cewa sun tsayu tsayin daka wurin tabbatar hadin kan Najeriya tare da cigabanta

Gwamnonin jihohi 17 na kudancin Najeriya sun shiga ganawa a jihar Delta dake kudancin kasar nan.

Hotuna cikin labari: Gwamnonin Kudancin Najeriya sun yi taro a Delta
Hotuna cikin labari: Gwamnonin Kudancin Najeriya sun yi taro a Delta. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

Wasu daga cikin gwamnonin da suka samu halartar taron sun hada da Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas, Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu, Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta da Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti.

Hotuna cikin labari: Gwamnonin Kudancin Najeriya sun yi taro a Delta
Hotuna cikin labari: Gwamnonin Kudancin Najeriya sun yi taro a Delta. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

A taron, ana tsammanin zasu tattauna a kan tsanantar rashin tsaro da ya addabi yankin da sauran halin da kasar ke ciki, Premium Times ta ruwaito.

KU KARANTA: Hadiza Bala Usman: Bani da ikon bada kwangila ni kadai a matsayina na manajan daraktan NPA

Hotuna cikin labari: Gwamnonin Kudancin Najeriya sun yi taro a Delta
Hotuna cikin labari: Gwamnonin Kudancin Najeriya sun yi taro a Delta. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kalubalen tsaro a Najeriya ya kusa zama tarihi, IGP ya jaddada

Hotuna cikin labari: Gwamnonin Kudancin Najeriya sun yi taro a Delta
Hotuna cikin labari: Gwamnonin Kudancin Najeriya sun yi taro a Delta. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

Gwamnoni 17 na jihohin kudancin kasar nan sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi jawabi ga 'yan Najeriya kan kalubalen tsaron kuma ya dawo da karfin guiwar jama'a.

Kungiyar ta sanar da hakan ne yayin da shugabanta, Olurarotimi Akeredelo na jihar Ondo ya karanto makasudin taron 12 a sa'o'i hudu na karshen taronsu a Asaba, babban birnin jihar Delta.

Gwamnonin sun tabbatarwa da jama'ar kudancin Najeriya cewa zasu cigaba da kokarin ganin hadin kan Najeriya dogaro da adalci da zaman lafiya tsakanin jama'a tare da fatan ganin cigaban tattalin arziki.

Gwamnonin sun yanke hukuncin hana kiwon dabbobi a tituna kuma sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi jawabi ga 'yan Najeriya.

A wani labari na daban, Gwamnatin tarayya ta bayyana Laraba, 12 da Alhamis 13 ga watan Mayun 2021 a matsayin hutun sallah karama mai zuwa.

Ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya bada wannan sanarwar a madadin gwamnatin tarayya a Abuja a ranar Litinin, The Nation ta ruwaito.

Ya taya Musulmi murnar zuwan sallah tare da kira ga 'yan Najeriya dake gida da ketare da su yi amfani da wannan lokacin wurin yin addu'ar zaman lafiya, daidaituwa da kuma habakar tattalin arzikin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel