Da duminsa: Rundunar 'yan sanda a Binuwai ta gano wasu kaburburan sirri

Da duminsa: Rundunar 'yan sanda a Binuwai ta gano wasu kaburburan sirri

- Rundunar 'yan sandan jihar Benue ta sake gano wasu kaburburan sirri a karamar hukumar Katsina-Ala

- Wasu miyagun 'yan ta'adda biyu da aka kama ne suka jagoranci jami'an tsaron da na karamar hukumar zuwa wurin

- An gano cewa Bob Tsetse mai shekaru 23 da Cash Money mai shekaru 22 sun addabi karamar hukumar amma sai dubunsu ta cika

'Yan sanda a jihar Binuwai sun bankado wasu kaburburan sirri a karamar hukumar Katsina-Ala ta jihar.

Daily Trust ta ruwaito cewa an samo ire-ire kaburburan nan a garin ZakiBiam dake karamar hukumar Ukum tun a watan Oktoban 2019, makonni uku bayan an gano wasu da ake zargin 'yan kungiyar asiri ne ke kashe mutane tare birnesu a ciki a karamar hukumar Ushongo ta jihar.

Wannan gano kaburburan da aka yi ya biyo bayan kama wasu miyagun gagararrun 'yan ta'adda biyu da aka yi wadanda ake zargin yaran Azonto ne, mataimakin marigayi Terwase Akwaza a yankin Katsina-Ala.

KU KARANTA: Kalubalen tsaro a Najeriya ya kusa zama tarihi, IGP ya jaddada

Da duminsa: Rundunar 'yan sanda a Binuwai ta gano wasu kaburburan sirri
Da duminsa: Rundunar 'yan sanda a Binuwai ta gano wasu kaburburan sirri. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Idanu sun zubda hawaye, Jalingo ta cika tankam yayin da aka yi jana'izar Mama Taraba

Ganau ba jiyau ba sun bada sunayen wadanda aka kama da Aondoaseer Terseer wanda aka fi sani da Bob Tsetse mai shekaru 23 da kuma Orkashima David mai shekaru 22 wanda aka fi sani da Cash Money.

Ganau din sun ce 'yan ta'addan biyu na daga cikin miyagun da suka yi shekaru suna addabar yankunan Mbamon, Tavachan, Michivhe duk a karamar hukumar Katsina-Ala amma sun tsere yayin da suka gane jami'an tsaro na nemansu.

Shugaban karamar hukumar Katsina-Ala, Alfred Atera, ya sanar da cewa an kama su ne a Illesa dake jihar Osun kuma an dawo da su jihar Benue.

Atera yace wadanda ake zargin a ranar Litinin sun jagoranci jami'an tsaro da wasu jami'an karamar hukumar zuwa inda suke tafka barnarsu a Katsina-Ala.

A wani labari na daban, Dan sanda mai mukamin DSP mai suna Abdulqadir Garba Hardo, wanda wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka harba a jihar Kebbi ya riga mu gidan gaskiya.

Hardo wanda 'yan bindiga suka harba a kafa yayin da yake jagorantar rundunar sun yi musayar wuta da 'yan bindigan a garin Tsamiya dake karamar hukumar Bagudo ta jihar.

Raunin da ya samu daga harsashin ya ratsa ta kashin kafarsa inda ya karya shi kuma ya rasu a wani asibiti dake Gusau, jihar Zamfara a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel