Tsohon Gwamnan Bayelsa ya fadi hanyar da Buhari zai yi maganin matsalolin kasar nan

Tsohon Gwamnan Bayelsa ya fadi hanyar da Buhari zai yi maganin matsalolin kasar nan

- Seriake Dickson ya yabi aikin da kwamitin APC ta yi a kana sake fasalin kasa

- Tsohon Gwamnan Bayelsa, ya yi kira ga shugaban kasa ya duba rahoton aikin

- Sanata Dickson ya na ganin rage karfin Shugaban kasa zai magance matsaloli

Sanata mai wakiltar yankin yammacin Bayelsa, Seriake Dickson, ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya duba batun sake yi wa Najeriya fasali.

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon gwamnan ya bayyana wannan ne a lokacin da aka yi hira da shi a wani shiri da aka yi a gidan talabijin na AIT a ranar Litinin.

Sanata Seriake Dickson ya ke magana kan kwamitin APC na sauya wa tsarin Najeriya zani da Nasir El-Rufai ya jagoranta, ya ce wannan aikin zai iya zama mafita.

KU KARANTA: Jama'a su yi ta addu'a a kan miyagu da masu satar mutane - Buhari

Seriake Dickson ya na ganin gwamnatin tarayya za ta shawo matsalar rashin tsaro idan ta yi wa dokokin kasa garambawul, ta yadda aka kara wa jihohin Najeriya karfi.

Dickson ya ce akwai bukatar shugaban kasa ya duba batun yi wa tsarin mulki kwaskwarima, wanda shi ne babban abin da duk ya jawo kalubalen da ake fuskanta.

A cewar Dickson, kundin tsarin mulkin 1979, ya ba gwamnatin tarayya karfin ikon da ya yi yawa, wanda hakan ya sa aka murkushe jihohi da kuma kananan hukumomi.

“Shugaban kasa ya na da karfin da ya yi yawa. Dole ya yi amfani da karfinsa, ya rike kasar nan.”

KU KARANTA: IGP ya tura 'Yan Sanda fiye da 4000 zuwa Kano

Tsohon Gwamnan Bayelsa ya fadi hanyar da Buhari zai yi maganin matsalolin kasar nan
Sanatan Bayelsa, Seriake Dickson Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Dickson ya ce: “Jam’iyyar shugaban kasa ta yi aiki mai kyau a bangaren canza fasalin kasa – akalla a waje mai muhimmanci, na rage karfin gwamnatin tarayya.”

“Kwamitin da gwamnan jihar Kaduna ya jagoranta, da Sanata Adetunmbi a matsayin Sakatare, da wasu ‘yan kwamiti sun yi aiki tukuru.” Inji Sanata Seriake Dickson.

A hirar da aka yi da shi, Dickson ya nuna ba ya goyon bayan kowani yanki ya kafa jami’an tsaro, ya ce abin da ya dace shi ne a hana makiyaya yawon kiwo da dabbobi.

A yau ne aka ji Ministan yaɗa labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ya bayyana cewa gwamnati ta san maɓuyar miyagun da suke satar mutane a ƙasar nan.

Lai Mohammed ya ce jami'an tsaro na sane da maɓuyar masu satar mutane, kawai suna bi a hankali ne domin kada su cutar da farar hula da ake fake da su a jeji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel