Ana Wanka da Kashin Shanu Saboda Tsoron Korona a Indiya

Ana Wanka da Kashin Shanu Saboda Tsoron Korona a Indiya

- Kungiyar Likitoci ta kasar Indiya ta yi gargadi a dena amfani da kashin shanu don maganin korona

- Wasu yan kasar mabiya addinin Hindu sun rika zuwa wurin da ake ajiye shanu suna shafe jikinsu da kashi da fitsarin shanun

- Dr JA Jayalal, Shugaban kungiyar likitoci na kasar ya ce babu hujja da kimiyya da ke nuna hakan na magani sai dai hatsari ma ke tattare da shi

Likitoci a kasar India suna gargadin mutane su dena amfani da kashin shanu a matsayin maganin COVID-19, inda suka ce babu wata hujja da kimiyya da ke nuna ingancinsa sai dai yada wasu cututukan, rahoton Reuters.

Annobar ta korona ta yi wa kasar India katutu inda a yanzu mutum miliyan 22.26 ne suka kamu sannan mutum 246,116 sun riga mu gidan gaskiya.

Ana Wanka da Kashin Shanu Saboda Tsoron Korona a Indiya
Ana Wanka da Kashin Shanu Saboda Tsoron Korona a Indiya. Hoto: @thecableng
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Rikicin Limanci: Gwamnati Ta Rufe Masallaci Bayan Limamai Biyu Sun Mutu a Osun

Kwararru sun ce ainihin adadin wadanda cutar ta halaka za su iya rubanya wannan adadin sau biyar ko 10 kuma yan kasar na fama da karancin gadon asibiti, magunguna, iskar numfashi na Oxyegen hakan yasa ake barin wasu suna mutuwa ba kulawa.

A jihar Gujarar da ke Yammacin India, wasu suna zuwa wurin kiwon shanu sau daya a mako su shafe jikinsu da kashi da fitsarin shanun da fatan hakan zai habbaka garkuwar jikinsu ko warkar da su daga cutar ta korona.

A addinin Hindu, shanu abin girmamawa ne kuma alama ce ta rayuwa da kasa, tsawon shekaru masu yawa Hindu suna amfani da kashin shanu domin goge gidajensu da kuma bauta, suna masu imanin cewa yana magance cututtuka.

Sai dai likitoci da masu nazarin kimiyya a kasar da duniya suna ta nanata gargadin cewa a dena hakan don magance korona, inda suka ce hakan na iya tsananta cutar ko kuma ya saka mutane su yi sakaci su kamu da ita.

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Ana Jin Ƙarar Harbin Bindiga a Yayin Da Boko Haram Ke Ƙona Gidaje a Maiduguri

"Babu wani hujja ta kimiyya da ke nuna kashi ko fitsarin shanu na inganta garkuwar jiki ko maganin Covid-19, kawai camfi ne," a cewar Dr JA Jayalal, shugaban kungiyar likitoci na kasar India.

"Akwai hatsari da ke tatattare da shafa ko cin irin wannan abubuwan - wasu cututtukan na iya tashi daga cikin dabobi su shiga mutane."

A wani labarin daban kun ji cewa gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin ta tabbatar da cewa mutane shida sun mutu sakamakon wata bakuwar cuta a karamar hukumar Minjibir a jihar, Vangaurd ta ruwaito.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Ibrahim-Tsanyawa wanda ya tabbatar da hakan ya ce wasu mutum 46 da suka kamu da cutar na jinya a asibiti.

Ibrahim-Tsanyawa ya ce cutar ta bulla ne a kauyen Gandun Koya da ranar 7 ga watan Mayu kuma ta yadu zuwa garuruwan da ke makwabtaka da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164