Labari da duminsa: Ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a Saudiyya

Labari da duminsa: Ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a Saudiyya

- Kasar Saudi Arabia bata ga jinjirin watan Shawwal ba a yau Litinin, 11 ga watan Mayu

- Kasar ta sanar da hakan ne a wata wallafa da tayi a shafin Haramain Sharifain a Twitter

- Hakan yana nufin za cika watan Ramadan zuwa talatin in da za a yi sallah ranar Alhamis

Kasar Saudi Arabia ta sanar da cewa ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a yau Litinin, 11 ga watan Mayun 2021. Hakan yasa za a cika watan Ramadan ya kai talatin inda za a yi sallah karama a ranar Alhamis, 13 ga watan Mayun 2021.

Tuni dai tawagar duban watan ta taru domin hangawa tare da gano jinjirin watan Shawwal kamar yadda Haramain Sharifain ta wallafa a shafinta na Twitter.

Sanarwar na nuna cewa rashin ganin jinjirin watan ya shafa kasar Saudi Arabia ne da dukkan kasashen dake bin ranaku irin nata.

KU KARANTA: Amaechi ya kafa kwamitin mutum 11 domin binciken Hadiza Bala Usman

Da duminsa: Ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a Saudiyya
Da duminsa: Ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a Saudiyya
Asali: Original

KU KARANTA: Hadiza Bala Usman: Bani da ikon bada kwangila ni kadai a matsayina na manajan daraktan NPA

A wani labari na daban, Usman Baba, sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, ya ce jami'an tsaro na aiki tukuru wurin tabbatar da cewa sun shawo kan matsalar tsaron kasar nan, The Cable ta ruwaito.

Baba, wanda ya samu wakilcin DIG Danmallam Mohammed, ya sanar da hakan ne yayin da ake yayen 'yan sandan da suka samu horo a bangaren shugabanci a kwalejin 'yan sanda dake Jos.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito, ya ce hukumar 'yan sanda na aiki tukuru wurin dawo da zaman lafiya a dukkan sassan kasar nan kuma tana hada kai da sauran hukumomin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng