Hadiza Bala Usman: Bani da ikon bada kwangila ni kadai a matsayina na manajan daraktan NPA

Hadiza Bala Usman: Bani da ikon bada kwangila ni kadai a matsayina na manajan daraktan NPA

- Dakatacciyar shugaban hukumar NPA, Hadiza Bala Usman, ta musanta rahotanni da ke yawo na cewa ita kadai ke iya bada kwangila a NPA

- Kamar yadda ta bayyana a wata takarda, ta ce wannan rahoton na nuna tsabar rashin fahimta, rashin tunani da son bata mata suna

- A cewar tsohuwar shugaban NPA, hukumar ta mallaki kungiya dake duba duk wani bangaren kasuwanci da kadarorinta

Hadiza Bala Usman, dakatacciyar manajan daraktan NPA ta musanta rahoton kafafen yada labarai na cewa ita kadai ke iya bada kwangila a hukumar yayin da take shugabanci.

A wata takarda da ta saka hannu a ranar Lahadi, 9 ga watan Mayun 2021, Usman ta kwatanta rahotannin da rashin fahimta tare da bacin suna, The Cable ta ruwaito.

A makon da ya gaba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da bala Usman a matsayin manajan daraktan NPA kuma ya amince da nada Mohammed Koko domin ya jagoranci hukumar har sai an kammala bincikenta.

KU KARANTA: Yadda aka yi amfani da kafar sada zumunta wurin fallasa Boko Haram a Kano

Hadiza Bala Usman: Bani da ikon bada kwangila ni kadai a matsayina na manajan daraktan NPA
Hadiza Bala Usman: Bani da ikon bada kwangila ni kadai a matsayina na manajan daraktan NPA. Hoto daga @TheCableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Buhari zai yi bikin sallah a fadar Aso Rock, yace baya bukatar gaisuwar sallah

The Cable ta ruwaito dalla-dalla yadda Rotimi Amaechi, ministan sufuri ya shiga ya fita har ya tabbatar da amincewar Buhari wurin dakatar da Bala Usman.

Bala Usman ta ce NPA tana da kungiya wacce koyaushe take yanke hukunci kan dukkan kadarorin da kasuwancin NPA kuma mai dogaro da ra'ayin 'yan Najeriya.

"Cewa ni kadai nake bada kwangila a matsayin manajan daraktan NPA, akwai son zuciya, rashin fahimta da kuma son bata suna," takardar tace.

A wani labari na daban, a daren Lahadi ne rundunar sojin Najeriya tace dakarun runduna ta 8 da aka tura yakar 'yan bindiga da suka addabi Zamfara da jihohi dake da makwabtaka dasu sun kashe kwamandojin 'yan bindiga 5 tare da wasu miyagu 48 bayan musayar wuta da aka yi.

Har ila yau, dakarun sun yi kokarin ceto mutum 18 da aka yi garkuwa dasu daga sansanin 'yan bindigan, Vanguard ta ruwaito.

Birgediya janar Mohammed Yerima, daraktan hulda da jama'a na sojin kasa, wanda ya sanar da hakan a wata takarda ya kara da cewa an tarwatsa sansanin 'yan bindiga masu yawa inda aka samo miyagun makamai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel