Za Ku Dandana Kudarku, Ba Ku Fi Karfin Gwamnati Ba, Lai Mohammed Ga 'Yan Bindiga

Za Ku Dandana Kudarku, Ba Ku Fi Karfin Gwamnati Ba, Lai Mohammed Ga 'Yan Bindiga

- Lai Mohammed ya bayyana cewa, ana kokarin sanyawa 'yan Najeriya tsoro ne kawai a kasar

- Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin tarayya da na isasshen karfin ragargazar 'yan bindiga

- Hakazalika ya bayyana yadda wasu bata-gari ke son ingiza kasar cikin halin rashin tsaro

Lai Mohammed, Ministan yada labarai da al'adu, ya ce 'yan bindigar da ke addabar kasar za su dandana kudarsu, TheCable ta ruwaito.

An samu matsalar yawaitar barnar 'yan bindiga a duk fadin kasar wadanda suka kai ga satar mutane tare da neman kudin fansa da kuma aikata fashi da makami.

Da yake jawabi a taron manema labarai a Legas a ranar Talata, Mohammed yace jami'an tsaron kasar sun fuskanci hare-hare na "rashin tunani" daga 'yan bindiga don cusa tsoro da haifar da rashin tsaro.

KU KARANTA: 'Yan Kasuwa Sun Tafka Asara Bayan Mummunar Gobara da Ta Yi Kaca-kaca da Kasuwa

'Yan Bindiga Basu Fi Karfin Gwamnati Ba, Zasu Dandana Kudarsu, Lai Mohammed
'Yan Bindiga Basu Fi Karfin Gwamnati Ba, Zasu Dandana Kudarsu, Lai Mohammed Hoto: thenationonlineng.com
Asali: UGC

Ministan ya ce sabanin ra'ayin wasu ‘yan kasar, gwamnatin tarayya ba ta dulmuye ba saboda kalubalen tsaro.

"Ina so in fada, ba tare da wata shakka ba, cewa duk wani hari kan jami'an tsaronmu maza da mata, hari ne kan kasar da kuma shelar yaki da al'ummar kasar,"

“Akan yi haka ne, saboda, a dulmuya karfin hukumomin tsaro. Yayin da wadanda suke da alhakin kare mu su kansu suke fuskantar hare-hare marasa tunani, hakan na faruwa ne saboda dalili daya kawai; Don cusa tsoro da haifar da rashin tsaro a tsakanin mutane.

"Ko sanannu ne ko ba a san su ba, wadanda ke aikata wannan mummunan aikin za su dandana kudarsu."

KU KARANTA: Saboda Ayaba, Wani Soja Ya Bindige Dan Kasuwa a Jihar Zamfara

A wani labarin, Fadar shugaban kasa ta nishadantar da 'yan kasa don saukaka mummunan yanayin da ‘yan Najeriya ke fuskanta na mawuyacin hali biyo bayan matsalar tsaro da ake ciki a kasar.

Wata mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Lauretta Onochie, a ranar Litinin, 10 ga Mayu, ta shawarci ’yan kasar cewa duk da cewa kasar na cikin mawuyacin hali, amma tuni Shugaba Buhari ya fara gyara dimbin matsalolin ta hanyar ayyukan gina kasa.

Onochie, wacce ta tuno da cewa marigayi Chinua Achebe ya rubuta wani littafi a baya mai taken 'There was a Nation', ta lura cewa babu wani abu sabo da zai zo da sauki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel