Allahu Akbar: Shekaru 14 da rasuwar Sheikh Jafar Adam, Yaronsa ya sa wa ‘Dansa suna Jafar

Allahu Akbar: Shekaru 14 da rasuwar Sheikh Jafar Adam, Yaronsa ya sa wa ‘Dansa suna Jafar

- Mai dakin Salim Jafar Mahmud Adam ta haifi yaro namiji a jiya

- Salim shi ne babban ‘Dan Marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam

- Angon karnin ya sa wa wannan jaririn sunan mahaifinsa, Jafar

A ranar Litinin, 10 ga watan Mayu, 2021, Malam Salim Jafar Mahmud Adam ya bada sanarwar cewa Mai dakinsa ta haihu.

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa wannan Bawan Allah ya samu baiwar ‘diya mace ne a daidai ranar 28 ga watan Ramadan, 1442.

A daidai lokacin da musulmai su ke shirin bankwana da watan Ramadan, sai aka ji Salim Jafar Adam ya samu karuwar namiji.

KU KARANTA: 'Dan marigayi Sheikh Jafar Mahmoud Adam ya rasu

Salim Jafar Adam wanda shi ne babban ‘dan Marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam, ya bada wannan sanarwa a shafin Twitter.

“Alhamdulillahi…Allah ya albarkacemu da jariri namiji (sunansa Ja’afar Ibn Saalim);” inji Salim a shafinsa na Twitter a ranar Litinin.

“Da jaririn, da mahafiyarsa, duk suna cikin koshin lafiya. Muna barar addu’o’i wajen saukin samun lafiyar mahaifiyar jaririn.

Daga baya, Salim ya yi wa jama’a godiya da irin addu’o’in da suka rika yi wa iyalinsa, da kuma mahaifinsa wanda ya yi wa takwara.

KU KARANTA: Ni na yi magana da Malam Jafar karshe kafin a kashe shi - Salim

“Assalamu alaikum, Nayi farin ciki matuka bisa ga addu’o’inku, da fatan Alheri, akan karuwa da muka samu, Allah ya saka muku da alheri.

“Allah ya amshi addu’o’inmu baki daya. Allah Ya kara Jikan malan, Ya kai rahama makwancinsa, Ya hada fuskokinmu baki daya a Aljannar firdaus.

A watan Yunin shekara bara ne matashin ya auri sahibarsa, Naja’atu Abdulaziz Abdullahi.

An yi wannan aure ne a kebabben yanayi saboda fama da ake yi lokacin da annobar COVID-19 a Najeriya da sauran kasashen Duniya.

Idan za ku tuna da-dama daga cikin manya-manyan Malaman da ake ji da su a Arewacin Najeriya sun halarci wannan daurin aure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel